✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Batanci ga Annabi: CAN ta fasa gudanar da zanga-zanga kan kisan Deborah

A maimakon haka, CAN ta bukaci a yi zanga-zangar a cikin majami’u

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bukaci mambobinta da su dakatar zanga-zangar da ta tsara yi ranar Lahadi kan kisan Deborah Samuel, dalibar da ta zagi Annabi Muhammad (S.A.W) a Jihar Sakkwato.

Shugaban kungiyar na kasa, Dokta Samson Ayokunle ne ya ba da umarnin a cikin wata sanarwa ranar Asabar.

A maimakon haka, kungiyar ta bukaci Kiristocin su gudanar da zanga-zangar a cikin majami’unsu ranar Lahadi.

Shugaban ya ce, “Kuna sane da cewa wasu Musulmai sun shelanta shirya tasu zanga-zangar ranar Lahadi, 22 ga watan Mayun 2022. Babban burinsu shi ne su tayar da zaune tsaye sannan su alakanta hakan da mu.

“Saboda haka, ina kiranku da ku gudanar da zanga-zangar ta hanyar daga kwalaye a harabar majami’unku da sakatariyar CAN da ke yankunanku.

“Sai dai a inda nan ma kuka fuskanci akwai matsala in kuka yi zanga-zangar a harabar majami’un naku, za ku iya daga kwalayen kawai a ciki, sannan ku yi wa Deborah Samuel addu’a.

“Sannan ku yi addu’a ga wadanda suke jin dadin kisan mutane ’yan uwansu da sunan addini,” inji Shugaban kungiyar Kiristocin.

Ya kuma bukaci majami’un da su kyale gidajen talabijin su dauki zanga-zangar sannan su yada ta a kafafen sada zumunta na zamani saboda duniya ta gani.