✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barkindo: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da tsohon Babban Sakataren OPEC

Aminiya ta zakulo muku abubuwan da za arika tunawa da shi

A ranar Laraba ce a ka wayi gari da sanarwar rasuwar Muhammad Sunusi Barkindo, Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC mai shirin barin gado.

Ya rasu ne wajen misalin karfe 11:00 na daren Talata, ‘yan sa’o’i bayan ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Ya rasu yana da shekara 63 a duniya.

Aminiya ta zakulo muku wasu abubuwa guda biyar dangane da marigayin da za a dade ana tunawa da shi.

  1. Shugabanci a kungiyar OPEC

Marigayin shi ne Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur – OPEC  mai barin gado, kuma na hudu a jerin shugabannin da suka rike wannan mukami daga Najeriya.

  1. Wa’adin shugabancinsa

Shekarar marigayi Barkindo shida yana rike da wannan mukami kuma wa’adinsa na Shugabanci zai kare ne a watan Agusta na shekarar 2022.

  1. Fafardo da farashin danyen mai a kasuwar duniya

Daya daga cikin nasarorin da marigayin ya samu a lokacin shugabancina shi ne farfado da darajar danyen mai a kasuwar duniya bayan da farshin ya fadi zuwa kasa da Dala 10 kan kowacce ganga sakamakon samar da wata yarjejeniya ta hadin kai da kasashen da ke ciki da kuma wajen kungiyar.

  1. Ganawa da Buhari a daren da zai rasu

Marigayi Barkindo ya rasu ne a daren Talata a Abuja, wasu sa’o’i bayan ganarwarsa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

  1. Sarautar Walin Adamawa

Marigayi Muhammad Barkindo har zuwa lokacin rasuwarsa shi ne yake rike da sarautar Wali Fombina na Adamawa.

Marigayin ya rasu yana da shekara 63 da haihuwa, ya kuma bar mata biyu da da daya.