✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dala 65m: ICPC na neman surikin Buhari ruwa a jallo

ICPC na neman Gimba Kumo da wasu mutum biyu ruwa a jallo kan kudaden gidaje.

Hukumar da Yaki da Ayyukan Zamba (ICPC) na neman surikan Shugaba Buhari, Gimba Kumo kan badakalar Dala miliyan 65.

Sanarwa da kakakin ICPC, Azuka Ogugua, ya fitar ta bukaci jama’a da su taimaka mata da bayanai da za su kai ga gano inda mutanen da take nema ciki har da surikin na Buhari suke, ko kuma su sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.

“Duk mai bayani kan inda mutanen suke dangane da kudaden samar da gidaje ga ma’aikata da suka handame, yana kai rahoto ga Hedikwatar ICPC da ke Abuja ko ofisoshinta a jihohi ko ofishin ’yan sanda mafi kusa,” inji sanarwar.

Kumo, tsohon Daraktan Gudanarwa ne, na bankin ‘Federal Mortgage’ ne lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

ICPC na neman mijin na ’yar Shugaba Buhari, Fatima, tare da Tarry Rufus da kuma Bola Ogunsola ruwa a jallo.

Sai dai har yanzu Fadar Shugaban Kasa ba ta ce uffan ba dangane da neman da ICPC ke yi surukin na Shugaban Kasa da sauran mutanen.