✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu san ranar sake bude makarantun da muka rufe ba – Gwamnatin Neja

“Ban san lokacin da za su koma makaranta ko ga lokacin sake bude makarantun ba”.

Gwamnatin jihar Neja ta ce bata san ranar sake bude makarantun kwanan da ta rufe a jihar ba saboda matsalar rashin tsaro.

Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Hajiya Hannatu Jibrin Salihu ce ta sanar da hakan ranar Lahadi, yayin da take damka daliban makarantar sakandire ta garin Kagara da aka kubutar ga iyalansu.

A cewarta, za su tattauna da iyaye, malamai da ma sauran masu ruwa da tsaki domin fito da nagartattun hanyoyin sake bude makarantun.

Ta ce, “Kalubalen tsaron dake fuskantar jiharmu ba karami bane, dole mu tabbatar da yin abin da ya dace kafin mu yi tunanin sake bude wadannan makarantun.

“Ba zan iya cewa ga lokacin da za su koma makaranta ko ga lokacin sake bude makarantun ba, amma muna nan muna shirye-shiryen ganin daliban aji uku na babbar sakndire bas u rasa jarrabawarsu ta kammala sakandire ba”.

Dagan an sai Kwamishiniyar ta yi kira ga daliban da kada lamarin da ya faru ya sare musu gwiwa, tana mai cewa za su koma yankunansu ne a matsayin jarumai.

Shima da yake jawabi, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Muhammad Makusidi ya tabbatarwa da daliban cewa gwamnati da kuma tsofaffin daliban makarantar za su hada karfi da karfe wajen ganin al’amura sun dawo kamar yadda ya kamata a makarantar.

A makon da ya gabata ne dai wasu ’yan bindiga suka sace dalibai da ma’aikatan makarantar ta Kagara a jihar ta Neja su kimanin 42 tare da hallaka daya daga cikinsu bayan ya yi yunkurin tserewa.