✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba kowane irin fim nake shiga ba — Tijjani Faraga

Tijjani Usman, wanda aka fi sani a masana’antar fina-finan Hausa da sunan Tijjani Faraga ba bako ba ne a duniyar fina-finan Kannywood da aka dade…

Tijjani Usman, wanda aka fi sani a masana’antar fina-finan Hausa da sunan Tijjani Faraga ba bako ba ne a duniyar fina-finan Kannywood da aka dade ana damawa da shi ba.

A cikin wannan tattaunawar da Aminiya ya tabo shigarsa harkar siyasa da kuma yadda yake gudanar da harkokin fim da kuma sauran batutuwa da dama.

Ko za ka fara da bayyna wa masu karatu ko wane ne kai?

Cikakken sunana shi ne Tijjani Usman wanda aka fi sani da Faraga a duniyar fina-finan Hausa na Kannywood.

Na fara karatun firamare a Jihar Filato kafin daga baya na karasa a Kurna ta Jihar Kano.

Yanzu haka ina da shaidar difloma a fannin koyon aikin jarida sannan, ina da takardar satifiket da na yi a kan shirya fina-finai a Cibiyar Koyar da Fina-finai da ke Jos. Ina da aure da ’ya’ya.

Ta yaya aka yi ka tsinci kanka a harkar fim?

Na fara ne da wasannin gidan talabijin tun kafin zuwan abin da a yau ake kira Kannywood ko kuma fina-finan Hausa.

Ina jin wannan horon da na samu ne ya ba ni damar taka rawar da nake takawa a matsayin furodusan fina-finai.

Bayan fara fina-finan Hausa da kafuwar masana’antar Kannywood, sai na fara samun kananan gurbi ina farawa da kadan da kadan har zuwa lokacin da wadanda suke kusa da ni irinsu Ali Nuhu suka shigo ciki tsundum, inda na fara samun dama a karin rawar da nake taka wa.

Da haka na fara na kawo matsayin da na ke a kai yanzu.

Ko ka samu lamarin da sauki kuwa?

Ka ga yawancin abin da mutane suka kasa ganewa shi ne nasara da daukaka ba a dare daya kawai ake samunsu ba.

Zan iya tuna wani lokaci na kan je wurin daukar shirin fim na kwashe tsawon kwana bakwai ina jiran samun gurbin da za a saka ni amma hakan bai kashe min kwarin gwiwana wajen ganin na cimma burina a masana’antar ba.

A sakamakon haka ga shi yau na kai inda na kai a harkar; cikakken dan wasa a Najeriya.

Ko za mu ji yadda ka samo sunan ‘Faraga’?

E, ba suna ne na wasan kwaikwayo da na samo a wasannin dabe ba. Lakabi ne da na samo daga wajen mahaifina yayin da nake karami.

A lokacin ina makarantar Islamiyya na kasance nakan zo na daya a cikin sa’anni na wajen haddar Al-Kur’ani.

Hakan ta sa mahaifina cikin farin ciki da jin dadi ta yadda duk lokacin da yake labarina ya kan siffata ni da yaro mai baiwa ta musamman (Faraga), wannan shi ne ma’anar sunan da kuma yadda na samo ta, daga nan sai mutane suka ci gaba da kira na Tijjani Faraga.

A kwanan nan ka shiga cikin harkokin siyasa, wannan na nufin Faraga ya bar shirya finafinai ke nan?

Kusan kowa ma dan siyasa ne da ya kan tsinci kan shi wani lokaci tsundum a cikinta.

Shiga ta harkar siyasa ba yana nufin na bar harkar fina-finai ba ne. Bari ma ka ji in takaita maka; gaskiyar magana ita ce a yanzu na fi tsunduma a fagen fina-finai fiye da a baya.

Shigata harkar siyasa ba ta saba da harkokin fina-finai ba, ina dai yin ta ne a matsayina na dan kasa mai cikakken ’yancin damawa a harkar.

Ina kokarin marawa wani dan siyasa baya ne wanda nayi amannar cewa idan har ya samu ragamar jahorancin kasar nan to zai fidd A’i daga Rogo, ba kowa ba ne face tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Adamu Mu’azu wanda bai bukatar wani dogon gabatarwa saboda kowa ya san irin aikin da ya yi a lokacin da yake gwamman jihar Bauchi.

Na yarda da kasancewar Najeriya kasa daya dunkulalliya shi ya sa na ke tallata dan takarar da zai tabbatar da wanzuwar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Ba ka tunanin a yi amfani da kai daga baya a zo a yi watsi da kai?

Ina sane da yadda wasu ’yan siyasa suka yi tutsun jaki da abokan aikinna ’yan fim a bayan sun yi amfani da su sun cimma burinsu. Sai dai duk da haka, Alhaji Adamu Mu’azu daban ne da sauran.

Mun riga mun daura damarar goya masa baya har zuwa karshe saboda fatar da mu ke da shi wanda sauran ‘yan kasa za su gani kurukuru kyawawan manufofinsa da muka hango.

Ko ka taba yin da na sanin kasancewarka dan wasan kwaikwayo?

Ban taba jin cewa abin da nake yi laifi ne ba. Hakan ta sa a matsayina na Musulmi kare addinina shi ne abu na farko da nake dubawa kafin tsare mutuncina sannan kare yankina na Arewa da kuma al’aduna.

A kowane lokaci na kan duba tare da tantance labarin da aka kawo min domin ganin ko ya dace na taka rawa a ciki.

A fili yake kowa ya san ba na boye matsayata kan duk irin labarin fim din da aka kawo min. Idan har akwai wasu kura-kurai a cikin na kan haskawa wadanda abin ya shafa idan sun gyara to, idan kuma ba alamat za su gyara sai na hakura da fitowa a cikin fim din.

Ko za ka iya bayyana mana ire-iren rawar da ka zabi fitowa a ciki?

Akwai irin rawar da na shawarci daya saga cikin abokan aiki na da kada ya kuskura ya fito a kai domin bai dace da mutum irinsa ba.

Ba na son ambaton sunan fim din amma wadanda suka sani sun san yadda ta kaya. A karshe bayan ya ki saurarona ya je yayi fim din sai dai a yanzu da fim din ya fito kasuwa ya fi kowa yin da na sanin fitowa a ciki da taka rawar da ya taka.

Mene ne ba za ka taba mantawa da shi ba a matsayinka na jarumi?

A matsayina na dan wasan da ya samu horo kuma na kwashe shekaru da dama a harkar fim, daya daga cikin abubuwan da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne lokacin da Sultan na Sakkwato ya gayyace ni gidansa a matsayin wani mutum mai muhimmanci.

Gaskiya duk lokacin da na tuna wannan na kan ji dadi da irin martabawar da yayi min. Ban taba tsammanin abubuwan da mu ke yi mutane irinsu na sanya ido ba.