✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Azumi da addu’o’i:  Boko Haram ta shiga ‘rudu’

Ta kashe kwamandojinta uku A ranar Litinin da ta gabata ce, al’ummar Jihar Borno da na wasu sassan kasar nan suka amsa kiran Gwamnan Jihar…

  • Ta kashe kwamandojinta uku

A ranar Litinin da ta gabata ce, al’ummar Jihar Borno da na wasu sassan kasar nan suka amsa kiran Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum na yin azumi da gudanar da adduo’i domin samun dawwamammen zaman lafiya da ganin bayan ta’addancin Boko Haram.

Gwamna Zulum ya bukaci haka ne, sakamakon hare-haren baya-bayan nan da ’yan Boko Haram  suka rika kaiwa a sassan jihar, inda ya ce ya kamata a dage da yin addu’o’i da azumi da Sallah domin yin hakan ne kawai zai iya kawo zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

Kiran Gwamnan ya samu karbuwa ganin yadda jama’a daga kowane sashi na al’ummar jihar da wasu jihohi suka bi sahu, kuma kwana daya sai ga labarin mayakan Boko Haram sun shiga rudu inda suka kashe wadansu kwamadojinsu uku.

Abin da ya sa muka amsa kiran Gwamna -Malamai

A Unguwar Bolori, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Bolori Sheikh Abubakar Gonimi  ne ya jagoranci gudanar da addu’ar, inda ya yi kira ga jama’a su ji tsoron Allah, kuma su gyara halayensu. Ya ce kiran da Gwamna Babagana Zulum ya yi babban abu ne, ya ce sun dade suna addu’a, amma yanzu sun kara samun karfin gwiwa, saboda sun samu shugaba mai adalci da sanin ya kamata da har ya yi tunanin bada umarnin a gudanar da azumi da addu’a, kuma hakan ya yi tasiri sosai ganin yadda jama’a suka karbi kiran.

Sheik Gonimi ya sake yin kira ga Musulmi su ji tsoron Allah, “Domin jin tsoron Allah ne kadai mafita daga dukkan wani hali na rashin zaman lafiya da kuncin rayuwa,” inji shi. Sai ya ce dama Allah Yana ba jama’a shugabanni ne daidai da irin halayensu, “Hakan ya sa ba mu da wani abu da ya kamata mu al’ummar Jihar Borno mun yi, illa mu ci gaba da yin addu’a da kuma kasancewa masu yin biyayya ga shugabanni. Domin Manzon Allah (SAW) ya ce ku yi biyayya ga shugaba, koda bawa ne, aka shugabantar a kanku,” inji shi.

Sheikh Abubakar ya tunatar da shugabannin cewa wannan shugabanci da Allah Ya ba su abin tambaya ne.

Wani mazaunin Maiduguri, Malam Muhammad Goni cewa ya yi hakika an gudanar da addu’a da azumi kamar yadda Gwamna ya nema, “Muna fata Allah cikin rahamarSa, zai amshi addu’o’inmu Ya ba mu zaman lafiya a Jihar Borno da Najeriya baki daya,” inji shi.

Ya ce, “Ya kamata al’ummar Jihar Borno mu kara gode wa Allah da Ya ba mu Gwamnan da yake kaunar jama’arsa, kuma a kullum burinsa a samu zaman lafiya mai dorewa a jihar, sannan mu ba shi duk goyon bayan da ya kamata, don ci gaban jihar da kasa baki daya.”

Shi ma Umar Ahmad da Aminiya ta tuntuba ya nuna farin cikinsa ne kan yadda jama’a suka amsa kiran Gwamnan, ya ce addu’a da ma ana yin ta, amma wannan umarni da Gwamna ya yi ya kara zaburar da mutane wajen tashi tsaye da yin addu’o’in zaman lafiya.

Sheikh Abubakar kyari wanda ya yi bayani kan muhimmancin azumin nafila don rokon Allah, ya ce yin azumi da addu’o’i za su taimaka sosai wajen samun zaman lafiya. Ya ce dama Musulmi ya kamata ya kasance kullum yana cikin addu’a, “To kuma sai ga shi shugaba ya umarci a yi haka, ka ga wannan ba karamin ci gaba ne, aka samu ba. Amma duk da haka ya kamata mu dage, mu gyara halayenmu, mu kyautata wa marayu da mabukata, mu kasance kullum bisa bin Sunnar Manzon Allah (SAW) wanda haka ne kawai mafita gare mu, daga halin da muka tsinci kanmu a ciki,” inji shi.

Ya shawaci jama’ar jihar cewa kada su dakata da yin addu’a da azumi kan wannan matsala.

Masallatai 30 suka gudanar da addu’o’i a Maiduguri

A masallacin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhussaini da ke Gwange, an gudanar da addu’o’in ne a karkashin jagorancin Assayid Sharif Abba Saleh tare da halartar mutane daga wurare daban-daban. An yi addu’ar ce  zagaye biyu ta farko da misalin  karfe 8:00  zuwa 11:00 na safe, sannan aka gudanar da ta biyu da karfe 4:00 na yamma har sai da aka yi buda baki.

Wata majiya ta ce an yi saukar Alkur’ani Mai girma 2, 522, sai Hasbunallahu miliyan 3 da dubu 245 da Lahaula miliyan 2 da dubu 670, Yasin dubu 26 Ya Ladifu dubu 500, Hailala dubu 60, Ya Kahharu dubu 40, Ya Salamu dubu 26 da sauransu.

Manyan malamai irin su Halifa Sheikh Ali Ahmad Abulfatahi da Sheikh Abubakar Gonimi da Sheikh Abba Ibrahim Saleh da Sheikh Muhammad Mustapha Mai ba Gwamna Shawara kan Harkokin Addini, sun yi ta kira ga jama’a su gudanar da azumi da addu’o’in, domin a samu zaman lafiya.

Aminiya ta samu labarin cewa a masallatai da fiye da 30 ne aka gudanar da addu’o’in da suka hada da Zawiyyar Sheikh Sherif Ibrahim Saleh da Masallacin Madinatu na Sheik Abulfatahi da Babban Masallacin Kofar Shehu da Masallacin Sheikh Gonimi da sauransu.

Mutanen gari sun ciyar da masu azumi abinci

Wani abin sha’awa shi ne yadda magidanta suka rika raba abinci da kunu da kayan marmari sadaka ga jama’a lokacin buda-baki bayan azumin.

A zagayen da Aminiya ta yi a wasu unguwannin birnin Maiduguri kamar Lamisula da Lawan Bukar da Shehuri ta Arewa da sauransu ta ga yadda aka rika dafa abinci da ababen sha ana ba mutane sadaka.

Jihohi sun bi sahu wajen yin azumi da addu’o’i

Kiran da Gwamna Zulum ya yi ba tsaya ga al’ummar Jihar Borno ko Arewa maso Gabas kadai ba, inda jama’a suka amsa kiran har ma a wasu jihohin Kudu.

Jihar Legas

A Jihar Legas an yi addu’o’i, inda Sarkin Barebarin Jihar Legas Alhaji Muhammadu Mustafa Mai Kanuri ya jagoranci addu’a ta musamman a Babban Masallacin Ijora da ke daura da Apapa a Legas.

Ya shaida wa Aminiya cewa baya ga azumin da suka yi a ranar Litinin sun shirya addu’a a ranar Talata inda aka tara malamai suka gabatar da saukar Alkur’ani sau 12. Ya ce jama’a da dama sun halarci addu’ar daga sassan Jihar Legas. “Mun yi addu’ar ce kamar yadda Gwamnan Jihar Borno ya bukata dama mu a nan Legas a Ijora mun dade muna shirya irin wannan addu’a, mun yi wa jiharmu ta Barno addu’ar samun zaman lafiya da kasa baki daya,” inji shi.

Jihar Ogun

A Jihar Ogun, Sarkin Barebarin Jihar Alhaji Muhammadu Gana Mai Kanuri na Ogun ya shaida wa Aminiya cewa ya jagoranci addu’ar ce a fadarsa da ke garin Shagamu, inda ya ce a ranar Litinin sun yi azumi sannan sun yi taron addu’ar a ranar Talata. “Mun hallara a fadata a nan muka yi addu’a, dama kuma a cikinta muke a koyaushe, fatarmu Allah Ya ba mu zaman lafiya a daukacin jihohin da ke fama da wannan matsala, kuma Ya yi mana maganin masifun da suke damunmu, Ya ba mu lafiya da zaman lafiya a kasarmu,” inji shi.

Aminiya ta gano cewa a jihohin Legas da Ogun, baya ga addu’ar da aka gudanar, mutane da dama sun yi azumin da niyyar a samu zaman lafiya a Jihar Borno da sauran jihohin kasar nan da ke fama da matsalar tsaro.

Jihar Bauchi

Da Aminiya ta leka Jihar Bauchi, mutane da dama sun yi azumi domin neman zama lafiya a Jihar Borno da Bauchi da Najeriya baki daya.

Sun ce sun yi wannan azumin ne don sun ji Gwamnan Jihar Borno ya yi umurni kuma ya nemi taimakon ’yan uwa su yi. Sun ce sun yi ne domin neman maslaha ga kansu saboda idan rikici ya ci Jihar Borno ko Adamawa ko Yobe to makwabtansu na kusa ne abin zai fara shafa.

Addaji Muhammad ta ce, “Tun kafin yau muna yin azumi, gaskiya muna so a daina kashe-kashe a samu zaman lafiya a sawwaka wa al’umma rayuwa, a samu aikin yi sai mu ji dadi.”

Sani Muhammad da ke Unguwar Makwalla ya ce, “Gaskiya mun ji dadin wannan azumi kuma mun ji Allah Ya karbi addu’o’inmu don mun ji labarin shugabannin Boko Haram suna fada a tsakaninsu.”

Jihar Adamawa

Wadansu daga cikin mutanen Jihar Adamawa sun gudanar da azumin samun zaman lafiyar.

Shugaban Kungiyar Musulmin Jihar Adamawa Malam Gambo Jika ya ce yana da masaniya a kan azumin da Gwamna Zulum ya umarta a yi, sai dai ya ce ba zai iya tantance yawan wadanda suka amsa kiran ba.

Malam Gambo ya ce yin azumi da rokon Allah abu ne mai kyau da zai amfani kowa. Ya ce akwai wadanda ya san sun same shi game da azumin, kuma sun fahimci abin da Gwamna Zulum yake nufi kuma sun gudanar da azumin.

Wani mai suna Malam Alhassan Haladu ya ce shi ya samu damar gudanar da azumin domin dama ya kasance mai yin azumin Litinin ne.

Abuja

A Abuja, Malam Muhammad Kabir Husri, ya ce bai yi azumin ba saboda hakan ba shi ne mafita ba. Ya ce matsalar da ke faruwa a Jihar Borno da Najeriya jarrabawa ce ga al’umma. “Saboda haka al’ummar wajen da gwamnatocinsu, halinsu ya kamata su kyautata. Su sun san abubuwan da suke yi marasa kyau, sai su daina. Sannan sun san wadanda suke yi masu kyau, sai su kara. A sunnar Manzon Allah (SAW) haka aka koyar. Kowa ya san Allah Ya albarkaci yankin da karatun Alku’ani Mai girma, amma maimakon su yi amfani da shi ta hanya mai kyau, sai mafi yawansu suka koma suna amfani da shi ta munanan hanya. Mu yi karatu kuma mu yi aiki da shi, wannan ne babbar mafita,” inji Malam Kabir.

Rikici ya barke tsakanin shugabannin Boko Haram

Jim kadan bayan gudanar da addu’o’in, sai aka samu labarin cewa rikici ya barke a tsakanin ’yan Boko Haram bangaren ISWAP da a da ke karkashin Al-Barnawi, wanda dan Muhammad Yusuf ne.

Rahotanni sun ce akalla manyan jagororin kungiyar uku aka kashe a rikicin da ya barke a tsakaninsu.

Idris al-Barnawi wanda shi ne jagoran Kungiyar ISWAP a Najeriya da Abu Maryam da Abu Zainab, wadanda su biyun ne aka ce sun jagoranci yi wa Abubakar Shekau tawaye, inda suka ware, duk an kashe su a rikicin na baya-bayan nan.

Wani masani kan harkokin Boko Haram, Barista Audu Bulama Bukarti ne ya fara wallafa wannan labari a shafinsa na facebook, inda ya ce, an kashe manyan jagororin ne bayan sun fara nuna sassauci.

Ya ce daga cikin sassaucin da suka nuna, sun bukaci a daina bin sojojin da suka gudu, sannan a daina kashe sojojin da suka kama.

“Wannan ya sa sauran jagorin suka ce manyan nasu sun yi sassauci sosai, inda hakan ya sa suka kashe su,” kamar yadda Bulama ya rubuta.

Wannan rikicin ya zo ne a makon da aka gudanar da addu’o’i domin samun zaman lafiya a Borno da kasa baki daya.

Idan ba a manta ba, Barista Bulama na cikin wadanda Abubakar Shekau ya yi wa kashedin ya daina abin da yake yi, ko kuma ya shiga matsala a makon jiya.

Sai dai a wani bincike da Premium Times ta yi tare da hadin gwiwar Humangle Media Foundation, suna ganin ba kashe Ba Idrissa aka yi ba, an aje shi a gefe ne.

“Abin da muke gani shi ne an ajiye Ba Idrissa (Idrisa al-Barnawi) ne a wani lungu a yankin Tafkin Chadi kamar yadda aka yi wa Abu Musab Al-Barnawi, wanda dan Muhammad Yusufwwwwww ne. Lokacin da aka kwace shugabanci a hannunsa, shi ma haka aka tsare shi na wani dan lokaci.”

Gwamna Zulum ya jinjina wa mutane

A sakonsa, Gwamna Babagana Zulum ya gode wa al’ummar Jihar Borno da na kasa baki daya, kan yadda suka amsa kiransa na azumi da addu’ar neman Allah Ya dawo wa jihar da zaman lafiya, da kuma Najeriya. Ya bukaci jama’a su ci gaba da yin addu’a da azumi har Allah Ya kawo karshen Boko Haram da ma dukkan ’yan ta’adda a fadin kasar nan.