✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayyukan da Buhari ya aiwatar a Spain kafin dawowarsa Najeriya

Tsawon shekaru da dama, Spain ta kasance daya daga cikin manyan abokan huldar kasuwanci da Najeriya.

A ranar Juma’a ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya daga birnin Madrid na Sifaniya bayan ya kammala ziyarar kwanaki uku.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, jirgin shugaban ya taso ne daga filin jirgin saman Torrejon da ke Madrid da misalin karfe 8:20 na safe agogon kasar zuwa filin jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

A ranar Laraba ce Buhari ya gana da Shugaba Pedro Sanchez da kuma Sarkin Spain, Mai Martaba Felipe VI.

A ganawar da suka yi da Shugaba Sanchez, Najeriya da Spain sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi guda tara ciki har da yarjejeniyar fahimtar juna da suka shafi ba da taimakon shari’a a kan batutuwan da suka shafi laifuffuka da musaya ko mika wadanda aka yanke wa hukunci ko wadanda ake tuhuma da aikata laifi.

Sauran batutuwan sun hada da al’amuran al’adu, hadin gwiwa wajen yaki da laifuka da inganta tsaro, da kuma batutuwan da suka shafi wadanda suka dogara da ma’aikatan da ke kula da harkokin diflomasiyya.

Ragowar kuma sun hada da hadin gwiwa a fannin makamashi, harkokin kasuwanci da zuba jari, bude ido, sufuri, kimiyya da kirkire-kirkire, kiwon lafiyar jama’a, yaki da annobar Coronavirus da kuma raya wasanni.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaba Buhari ya halarci wani taron Shugabannin Siyasa da ’Yan kasuwa, wanda kungiyar ’yan kasuwa ta kasar Spain, da Ma’aikatar kasuwanci, da Kungiyar Masu Daukan Ma’aikata suka shirya.

A wajen taron, shugaban na Najeriya ya ja hankalin kasashen Turai da su sa ido a kan nahiyar Afirka domin magance kalubalen da nahiyar ke fuskanta wajen samar da albarkatu ga kasashe wanda a halin yanzu ya shafi tattalin arzikin duniya baki daya.

Ya kuma kalubalanci masu zuba jari ’yan kasar Spain da su yi amfani da sauki da Najeriya ke da shi na rashin tsawwala biyan haraji domin bunkasa kasuwancin da tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

A cewarsa, tsawon shekaru da dama, Spain ta kasance daya daga cikin manyan abokan huldar kasuwanci da Najeriya.

Ya ce kasar Spain ta kasance kan gaba wajen sayen danyen man Najeriya, inda ya ce darajar kayayyakin da Najeriya ta rika fitarwa zuwa kasar Spain a shekarar 2020 kadai sun kai dala biliyan 4.8 yayin da kayayyakin da Spain ke fitarwa zuwa Najeriya ya karu daga dala miliyan 97.2 a shekarar 1995 zuwa dala miliyan 517 a shekarar 2020.

Haka kuma a ranar Alhamis din da ta gabata, shugaba Buhari ya karbi bakuncin wakilan al’ummar Najeriya mazauna kasar Spain da suka hada da kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa da wasu ‘yan kasuwar Spain masu sha’awar zuba jari a  Najeriya.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da ke gudanar da halastattun harkokin kasuwanci a kasashen waje da su rika zuba jari cikin hikima a gida wanda zai zama wani bangare na gudunmawar da suke bayarwa wajen kawo sauyi ga tattalin arzikin kasa.

Tawagar ‘yan Najeriya mazauna Spain da suka gana da shugaban sun hada da John Bosco, shugaban kungiyar ‘yan Najeriya a kasar Spain da mataimakinsa Richard Omoregbe.

Sauran sun hada da Kenneth Omeruo dan wasan Super Eagles da ke buga kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Leganes FC a  Madrid da kuma Obinna Okafor, wani wakilin kwallon kafa.

Buharin ya kuma ya shaida wa ‘yan Najeriya mazauna kasar shaidar da jakadun Najeriya a kasar Spain suka bayar a kansu na cewa sun kasance masu bin doka da oda a kasar ta Turai.

Daga cikin tawagar da ta yi wa Shugaba Buhari rakiya daga nan Najeriya ta kunshi akalla ministoci bakwai da suka hada da; Ministan Harkokin Ketare, Geoffrey Onyeama; Atoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN); Ministan Masana’antu, Cinikayya da Zuba Jari, Otunba Adeniyi Adebayo; Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed; Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola; Ministan Matasa da Raya Wasanni, Sunday Dare; da Karamin Ministan Lafiya, Olorunnimbe Mamora.

Sauran ’yan tawagar sun hada da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (rtd); Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da kuma Shugabar Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa.