✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Attajirin duniya, Jeff Bezoz, zai je duniyar wata

Hamshakin attajiri dan kasar Amurka, Jeff Bezos, zai je duniyar wata a cikin kumbon farko mai dauke da mutane da dama wanda kamfaninsa na Blue…

Hamshakin attajiri dan kasar Amurka, Jeff Bezos, zai je duniyar wata a cikin kumbon farko mai dauke da mutane da dama wanda kamfaninsa na Blue Origin ya kera.

Bulaguron an tsara yin sa ne ranar 20 ga watan Yuli, kwana 15 kafin Jeff Bezos ya sauka daga mukamin Babban Jami’in Kamfanin Amazon.

Kamfanin Blue Origin ya ce kanin attajirin, Mark Bezos, shi ma zai shiga ayarin wan nasa zuwa duniyar watan a cikin kumbon mai suna New Shepard.

Bezos mai shekara 57, ya wallafa shafin Instagram cewa, “Tun ina dan shekara biyar nake mafarkin tafiya zuwa duniyar wata.

“A ranar 20 ga watan Yuli, zan yi wannan babban bulaguron tare da kanina kuma babban aminina.”

Idan komai ya tafi daidai, Bezos zai zama biloniya na farko da ya zuba miliyoyin daloli a harkar tafiya zuwa duniyar wata ya kuma shiga kumbon da aka kera masa domin zuwa can.

Yawan dukiyar Mista Bezos, wanda shi ne ya fi kowa kudi a duniya,  ta kai Dala biliyan 187 kuma ya kafa kmafanin Blue Origin ne a shekarar 2000.

Blue Origin ya ya gudanar da gwaje-gwaje fiye da 12 na aika kumbon amma ba tare kowa a cikinsa ba, daga inda kamfanin yake da zama a wani kauyen Jihar Texas.

Bayan shekara shida ana ta gwajin New Shepard cikin sirri, kamfanin Blue Origin ya sanar a watan Mayu cewa yana shirye-shiryen daukar fasinjoji a cikin kumbon zuwa duniyar wata.

Shi ma attajiri Elon Musk, wanda kamfaninsa na SpaceX ya kera manya-manyan kumbon da za su iya shawagi zuwa duniyar Orbit daga nan doron duniyarmu, ya sanar da shirinsa na yin bulaguron zuwa duniyar watan a cikin kumbon da kamfaninsa zai kera.

Attajirin ya kafa kamfanin Amazon a 1994 da Dala dubu 250 da ya samu daga iyayensa, da farko a zaman shagon sayar da littatafai ta intanet.

Ko bayan ya sauka daga shugabancin kamfanin na Amazon, Jeff Bezos, ba zai tsame hannunsa gaba daya daga harkokin kamfanin ba inda zai ci gaba da aiki a zaman Shugaban Zartarwar kamfanin.

Andy Jassy, wanda shi ne Shugaban harkokin intanet na kamfanin zai gaje shi a kujerar Babban Jami’in Kamfanin na Amazon.