✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU za ta daukaka kara kan umarnin kotu na komawa bakin aiki

ASUU ta ce tuni ta fara hada kan manyan lauyoyinta

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta ce za ta daukaka kara kan umarnin da kotu ta bai wa mambobinta na su koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.

A ranar Laraba ce dai Kotun Ma’aikata ta Kasa ta malaman jami’o’in umarnin komawa bakin aiki har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Tarayya ta maka su a gabanta.

Amma ASUU ta ce ta soma hada kan jiga-jigan lauyoyi karkashin jagoranci babban lauyan nan, Femi Falana don su wakilce ta wajen daukaka karar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ran Laraba, shugaban ASUU na shiyyar Legas, Adelaja Odukoya, ya yi kira ga mambobin kungiyar da su kwantar da hankalinsu sannan su hada kai su ci gaba da wannan gwagwarmayar har zuwa karshe.

Tun farko, an rawaito Shugaban ASUU na Kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke na cewa,  za su zauna su tattauna kan umarnin da kotu ta ba su na su koma bakin aiki.

Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta soma wannan yajin aikin ne ran 14 ga Fabrairun da ya gabata da zummar neman hakkokinta a wajen Gwamnatin Tarayya.