✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asusun UNICEF ya yaba wa gwamnatin Bauchi kan kebe kashi 16 na kasafinta ga kiwon lafiya

Asusun Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) ya yaba wa Gwamnatin Jihar Bauchi kan kasancewarta jiha tilo a Najeriya da ta sadaukar da kashi 16…

Asusun Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) ya yaba wa Gwamnatin Jihar Bauchi kan kasancewarta jiha tilo a Najeriya da ta sadaukar da kashi 16 cikin 100 na kasafin kudinta na bana ga harkokin kiwon lafiya. Babban Jami’in Asusun da ke Bauchi, Abdullahi Kaikai ne ya bayyana haka a yayin da yake jawabi wajen bude bitar wuni biyu kan dabarun bunkasa ayyuka ga ’yan majalisar dokokin da suka fito daga jihohin Arewa maso Gabas a Gombe ranar Talatar mako jiya.

kungiyar ’Yan Majalisa don Fadada Kiwon Lafiya a Duniya (UHC) ta shirya taron, kuma daga cikin manufarsa akwai zurfafa fahimta kan dokokin da suka shafi samar da kudin kiwon lafiya da kula da lafiyar duniya da kuma bunkasa shirin da dokokin kiwon lafiya.

Kaikai, wanda ya samu wakilcin Misis Philomena Irene, wata kwararriya kan abinci mai gina jiki, ya ce taron kara wa juna sanin ya zo a daidai lokaci, ganin majalisun dokoki na jihohi za su duba ci gaban da aka samu kan halin da ake ciki game da gudasnar da ayyuka da tsare-tsare don inganta lafiyar mata masu juna biyu da abinci mai gina jiki ga yara a kasar nan. Ya ce ce rashin abinci mai gina jiki yana karuwa a Najeriya, inda wani bincike da aka gudanar kwanan nan ya nuna cewa an samu karin mutuwar yara daga kashi 24.2 zuwa 31.5, kuma jikkatar yaran ya karu daga kashi 34.8 zuwa 43.6. Kaikai ya ce kusan rabin mutuwar yara a Arewacin Najeriya na da alaka da rashin abinci mai gina jiki.

“Hakkin samar da abinci da abinci mai gina jiki, babban hakki ne domin tabbatar da rayuwar yara da kuma samar da ci gaban al’umma da kuma ita kanta kasar,” inji shi.

Ya ce:  “Samar da abinci mai gina jiki yana da matukar amfani domin tabbatar da nasarar shirin Ci gaba mai dorewa (SDGs) musamman wadanda ke da alaka da yunwa da lafiyar yara da mata masu juna biyu da samar da abinci da kuma ilimi.”

Kaikai ya kara da cewa zuba jari a bangaren samar da abinci mai gina jiki yana bukatar kudi sosai, amma kuma zai taimaka wajen magance matsalar da ake samu, kuma ya habbaka kudin shigar kasa, inda ya nanata cewa rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa “A duk Naira 1,000 da aka zuba a bangaren samar da abinci mai gina jiki, za a samu ribar Naira 16,000.” Ya bayyana ’yan majalisar a matsayin masu matukar muhimmanci wajen tsara kasafi da kafa doka da tabbatar da rikon amana da sanya ido domin ganin an inganta lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara, kuma ya bukaci so mayar da hankali wajen samar da isassun tanade-tanade a kasafin kudin jihohi na 2018.