A ranar Litinin 18 ga Disamban 2017 ne Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku ya aza tubalin gina Makarantar Sakandaren Gwaji a Takum Jihar Taraba da Asusun Tallafa wa wadanda bala’i ya shafa (bSF) ya dauki nauyin ginawa.
Babban Daraktan Asusun bSF, Farfesa Sunday Ochoche ya ce gina makarantar gwajin wata manuniya ce da ke nuna an yarda cewa jihar ma ta hadu da ta’addancin Boko Haram, wanda ya jawo kwararar dimbin ’yan gudun hijira kuma hakan ya kawo karancin kayayyakin inganta rayuwar jama’a a jihar.
Ya ce Asusun bSF ya ware Naira biliyan 1 da miliyan 250 don gudanar da wannan aiki, kuma ana sa ran za a kammala ginin a cikin watanni takwas.
A jawabin Gwamna Darius Ishaku ya ce gwamnatinsa ta yi maraba da yadda asusun ya zabi garin Takum wajen gina wannan makaranta, wadda ya ce idan aka kammala ta ba ma kawai za ta tallafa wa shirin sake fasalin ilimi da gwamnatinsa ke yi ba ne, har ma za ta taimaka wajen bai wa daliban da suke da matsala a jarrabawarsu ta sakandare ta hanyar bullo da karatun share fage domin su hanzarta samun gurabe a jami’o’i.