✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta cije kan Mudyryk, ana shirin cefanar da United, Depay zai ci gaba da zama a Barcelona 

Chelsea za ta iya sayen dan wasan gaban Faransa Marcus Thuram.

Arsenal na da kwarin gwiwar cewa za ta kammala cinikin fam miliyan 80 na sayen dan wasan Ukraine Mykhailo Mudyryk, don ta samu damar saka shi wasan da za ta yi da Manchester United mako mai zuwa.(Times)

Newcastle ta nuna sha’awar sayen dan wasan tsakiyar Portugal Ruben Neves, wanda watanni 18 suka rage masa a kwantiraginsa da Wolves, in ji jaridar Mail.

Chelsea ma za ta iya sayen dan wasan gaban Faransa Marcus Thuram kan yuro miliyan 10 kacal, don kwantiraginsa da Borrusia Monchegladbach za ta kare a karshen kaka, a cewar jaridar Caught offside.

Liverpool ta tattauna da wakilan Sofyan Amrabat na Maroko, to amma dan wasan tsakiyar na Fiorentina ya fi son tafiya Atletico Madrid, in ji Mirror.

Chelsea da Tottenham sun kyalla idon kan dan wasan gaban Belgium Leandro Trossard, bayan da wakilinsa ya fitar da sanarwa cewa dan wasan na son barin Brighton. (Football.London)

Manchester United ta samu tayi daga masu sha’awar sayen kungiyar daga Gabas ta Tsakiya, da Asiya da kuma Amurka.

Haka ma ana sa ran hamshakin mai arzikin nan dan Birtaniya, Sir Jim Ratcliffe, zai taya kungiyar. (Telegraph)

A nan kuma Wolves ce ta cimma yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiyar Brazil Joao Gomez daga kungiyar Flamengo. (Fabrizio Romano)

Sai kuma Manchester United, wadda tace dan wasan tsakiyarta Scott McTominay ba na sayarwa bane yanzu, duk da sha’awar daukar dan Scotland din da kungiyoyin Everton, da Southampton da Leeds, da West Ham, da Leicester suka nuna. (90min)

Chelsea ta ce tana goyon bayan kocinta Graham Potter, kuma tana shirin yin tankade da rairayar yan wasa, matsawar sakamakon da take samu a wasanni bai sauya ba. (Telegraph)

Ita kuwa Barcelona ta ce ba matse take ta sayar da Memphis Depay ba, kuma tana farin cikin ci gaba da aiki da shi har zuwa sadda kwantiraginsa za ta kare a karshen kaka. (Athletic)