✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Arewacin Najeriya Zai Kasance A Yanayin Hazo Na Kwana 3 —NIMET

Hukumar ta shawarci kamfanonin jirage da su dage da bibiyar hasashen yanayi a gudanar da ayyukansu.

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NIMET) ta yi hasashen cewa wasu sassan Najeriya za su kasance cikin yanayin hazo da rana daga ranar Laraba zuwa Juma’a.

Cikin wata sanrwa da hukumar ta fitar ranar Talata, ta ce Arewacin Najeriya baki dayansa da wasu jihohin Kudanci za su iya kasancewa cikin yanayin hazo da hasken rana jifa-jifa a wadannan kwanakin.

“Za a samu hazo da kuma hasken rana a biranen da ke kusa da ruwa a Kudancin Najeriya, yayin da jihohin Ondo, Akwa Ibom, Kuros Riba, Legas, Edo, za su iya samun ruwan sama da tsawa a ranakun Laraba da Alhamis.

“Shi kuwa yankin Arewacin Najeriya ranar Alhamis kuma, zai kasance cikin rana da hazo, yayin da dukkanin sassan kasar zai fuskanci sanyi da daddare a kwanakin”, a cewar sanarwar.

Hukumar ta shawarci kamfanonin jirage da su dage da bibiyar hasashen yanayi a gudanar da ayyukansu.