✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC da PDP sun yi wa Mamman Daura Raddi

Jam’iyya mai mulki ta APC da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, sun ce suna nan kan turbar mulkin karba-karba a zaben shekarar 2023. Wannan martani…

Jam’iyya mai mulki ta APC da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, sun ce suna nan kan turbar mulkin karba-karba a zaben shekarar 2023.

Wannan martani ne ga kira da na hannun damar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wato Mamman Daura ya yi a ranar Talata cewa a bi cancantar dan takara ba daga ina ya fito ba.

Daura ya kara da cewa an yi mulkin karba-karba fiye da sau uku amma bai haifar da da mai ido ba.

Daura na ‘yancin ra’ayimsa

Jam’iyyar APC, wadda kawun Mamman Daura ya lashe zaben shugabancin kasa karo na biyu a karkashinta ta yi fatali da batun cancantar.

Babban Sakatarenta na Watsa Labarai na jam’iyyar, Yekini Nabena, ya gaya ma wakilinmu ta wayar tarho cewar za su gudanar tsarin karba-karba idan lokacin ya yi.

“Wannan ra’ayin Mamman Daura ne kuma kowa yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa. Kuma haka nake son siyasa ta kasance.

“Akwai mutane da dama da suka kawo ra’ayoyi daban-daban kan wannan batun. Amma bai zama wani abun damuwa ba.

“Jam’iyya za ta zauna ta tsara yadda karba-karbarta zai kasance kamar kowacce jam’iyya. Wannan ba matsala ce ba”, inji Nabena

Za mu karba-karba in lokaci ya yi

A nata martanin, Jam’iyyar PDP ta bakin Mataimakin Sakataren Watsa labaranta, Deran Adeyemi, cewa ta yi, kiran da Daura ya yi na a bi cancanta bai zama wahayi ga jam’iyyar ba.

“Ra’ayinsa ne, kuma bai zama dole PDP ta yi amfani da shi ba saboda PDP jam’iyya ce da ta dauki karba-karba da muhimmmanci.

“Don haka idan lokaci ya yi, dole mu gabatar da tsarin karba-karba wanda zai bayyana daga ina Shugaban Jam’iyya zai fito, da kuma yankin dan takarar shugabancin kasa zai fito,” inji shi.