✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ango ko Iyayen Amarya: Wa ya fi dacewa ya yi kayan daki?

Wasu na ganin dacewar iyayen amarya su yi mata kayan daki don tsare mata mutunci.

Bisa al’adar yawancin al’ummomin Arewacin Najeriya, akan kai amarya dakin miji ne da kayan dakinta da iyayenta suka yi mata, kama daga gado da katifa, kujeru da kayan girki da sauran kayan daki da na aikace-aikacen yau da kullum.

Shi kuma ango a bangarensa, baya ga biyan kudin sadaki da na toshi da dangoginsu, zai kai wa amaryarsa kayan lefe, ya kuma samar mata gida da sauran abubuwan da ba za a rasa ba.

Ra’ayoyin mutane dai sun bambanta game da wannan al’ada, inda wasu ke ganin hakkin miji ne, a matsayinsa na mai gida, ya samar wa matarsa duk abubuwan bukatar yau da kullum, kama daga wurin kwana zuwa kayan daki da kayan abinci da kayan alatu da sauran kayan amfani.

Wasu kuma suna ganin hakkin iyayen amarya ne su yi wa ’yarsu kayan daki, har da na gara, domin hakkinsu ne su tabbatar da ta je dakin mijinta da mutuncinta ba tare da wata karanta ba, ballantana gori ya biyo baya idan aka samu sabani.

Wa ya fi dacewa ya yi?

Aminiya ta tattauna da wasu mutane domin jin ra’ayoyinsu kan wannan al’ada ta iyaye su yi wa ’ya’yansu da suka aurar kayan daki.

Shin hakkin iyayen amarya ne su yi mata, ko kuma hakkin mijinta, ango?

Anas Soba ya ce, “Shi kayan daki dangin amarya ke yin sa, ango da danginsa kuma akwati da kudin sadaki suke bayarwa.

“Yawancin dangin amarya ba sa yarda su karbi kayan daki daga wurin dangin ango saboda tsoron abin da zai je ya dawo na gori da fadin bakaken maganganu,” a cewarsa.

Sani Muhammad Nasidi, “Duk yadda ya zo mun; In ta ce za ta yi to ba matsala, amma in ta ce ba za ta yi ba, to ni zan yi mata.”

Ya ci gaba da cewa, “In kuma shi angon mai kudi ne kuma ya san cewa dangin yarinyar ba su da halin da za su yi mata kayan daki, to sai ya yi mata, saboda wannan abun al’ada ne.”

Shi kuma Muhammad Kabir Jaji ya ce, “Al’adar kasar Arewa ce, domin wasu yarukan kamar Yarubawa da sauransu in aka tashi kawo mace, ita kawai za a kawo maka.

“Al’adar mutanen Arewa ce idan ka auri mace a kawo maka ita da gado da katifa, a yi mata kaya [na daki] da sauran abubuwa.

Illar yin kayan daki

“Wannan al’ada ta mutanen Arewa ce ta sa wanda zai aurar da ’ya mace ya fi kowa wahala [idan bikin ya taso],” kamar yadda Muhammad ya bayyana.

Sai dai ya ce, hakan “Yana daga cikin dalilan da suka sa ake yawan yin sakin aure a Arewa, saboda in da namiji ne yake shan wahala sosai ya biya kudin gida, ya sayi kayan daki, ya biya sadaki, sai a kawo mishi mace kuma a ce idan ya sake ta, za ta tafi da duka kayan da ya saya, wannan zai sa shi ganin darajanar aure kuma ba za a rika yawan saki ba.

“Amma duk da wannan al’amari da ake yi [na al’ada], in aka je daurin aure sai ka ji [liman na bayyana cewa] ci da sha da fatarwa da wurin kwana da kare mutunci da koyar da ilimi sun tashi daga kan iyayenta sun koma kan mijinta.

Dambarwar kayan gara

“Akwai wani abun da ake kira gara, wanda iyayen amarya suke yi bayan sun aurar da ita.

“Wannan al’ada ita take sa duk mai ’ya’ya mata shiga cikin zullumi saboda irin kudaden da zai kashe wajen yi musu gara sun yi yawa.

“Mace ko da ’yar talaka ce za ta yi aure a kasar Arewa sai a kashe akalla N500,000 a wurin sayen kayan daki, sadaki kuma daga 50,000 zuwa 100,000 ne.”

‘Ya yi kayan daki yadda yake so’

Khadija Ali ta ce ita tafi son namiji ya yi kayan daki yadda yake so, saboda shi zai iya sanin abun da ya kamata a sa a daki.

A cewarsa, a sonta, shi ne kar ya kawo kayan lefe da kayan sa rana, sadaki kawai ta fi so. Amma ya bar mata kayan girki, ita za ta yi da kanta.

Patience Abba, ta ce ba laifi mace ta kawo kayan daki, saboda hakkin miji shi ne ya gina gida sannan ya dauki nauyin shirye-shiryen aure.

Ta ce a addinin Kirista bangaren miji suke shirya bikin, idan kuma dangin amarya suna masu kudi ne suna iya taimaka mishi.

“Don haka, al’adarmu ta yi wa miji adalci saboda mata ke zuwa gidan miji da kayan daki domin rage masa kashe kudade; Abu mafi muhimmanci dai shi ne ta zo da kayan ‘kitchen’ dinta.

Yayin da wasu ke ganin hakkin na miji ne, wasu kuma suna ganin cewa hakkin mace ne.

Hakan ya sa a wadansu yankunan Arewa, idan amarya ba ta zo da kayan dakinta ba, ba a daukar ta a matsayin amarya, duk da cewa idan auren ya rabu, kayan dakin sun zama nata.

Wasu matan kan sayar da kayan don samar wa kansu da ’ya’yansu abin dogaro.