✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Andrea Pirlo ya ajiye aikin horaswa a Turkiyya

Karagumruk tana ta tara a teburin gasar Turkiya ta Super Lig.

Andrea Pirlo ya ajiye aikin horar da kungiyar kwallon kafa ta Turkiya, Fatih Karagumruk.

Pirlo ya ajiye aikin ne yayin da ya rage saura wasa uku a kammala kakar bana.

Mai shekara 44 ya koma Istanbul a cikin watan Agusta, wanda ya yi fatan daga darajarsa a kungiyar, bayan da Juventus ta kore shi a 2021.

Kungiyar ta Turkiya ta sanar cewa mataimakin Pirlo, Alparslan Erdem, ya karbi aikin zuwa karshen kakar nan.

Pirlo, wanda ya karbi aikin yarjejeniyar kaka daya, ya lashe Champions Leagues biyu da Serie Ashida a lokacin da ya taka leda a AC Milan da Juventus.

Yana kuma cikin ‘yan wasan da suka lashe wa Italiya kofin duniya a 2006.

An sanar da nada Pirlo kociyan Juventus a cikin watan Agustan 2020, wanda ya ja ragamar kungiyar Turin ta lashe Italian Cup.

Sai dai an kore shi a 2021, bayan da Juventus ta fice daga Champions League a zagayen ‘yan 16 da yin ta hudu a teburin Serie A.

Hakan ne ya sa Juventus ta kasa daukar babban kofin tamaula na Italiya, bayan da ta ci tara a jere.

Kawo yanzu, Karagumruk tana ta tara a teburin gasar Turkiya ta Super Lig, wadda saura karawa uku a kammala wasannin bana.