✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana farfaganda ne kawai da fadan Fulani da Makiyaya – Kungiyar Zaman Lafiya

Wata kungiya mai zaman kanta (Rights Without biolence) a Zariya ta bayyana rashin gamsuwarta bisa yadda wasu rukuni suka maida rikicin manoma da makiyaya na…

Wata kungiya mai zaman kanta (Rights Without biolence) a Zariya ta bayyana rashin gamsuwarta bisa yadda wasu rukuni suka maida rikicin manoma da makiyaya na addini da kabilanci, wanda hakan ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba.

Da yake bayani ga taron manema labarai a Zariya, jagoran kungiyar Dokta Ahmad Jibrin Sulieman Garin Ali ya ce masu ruruta wutar rikicin sun fake da guzuma ne suna harbin karsana, domin kuwa a kasar nan kowa ya sani cewa akwai wadanda suke cin riba ta hanyar hada rigingimu, domin yau fiye da shekaru ishirin ke nan za ka ji ana cewa dan Najeriya ya kashe dan uwansa dan Najeriya saboda abin da bai taka kara ya karya ba.

“Dalilin haka muka yi kira ga gwamnati cewa da ta dauki matakai. Mun duba mun hango cewa matsalar da ake cewa yake-yake ne tsakanin manoma da makiyaya, bincikenmu ya nuna mana cewa abin fa ya wuce duk inda ake zato, domin ai ba kabilar Fulani ne suka haifar da rikicin Zagon Kataf ba kuma ba shi ya haifar da na Kafanchan ba, kuma ba shi ya kawo fadan garin Jos ba, haka kuma yakin da ake ta yi a Ebbe, shekaru wajen goma sha ake ta kawo masu hari, ba Fulani ba ne da Tibi, haka kuma fadan Mambila, ba Fulani da Bacama ba ne, haka kuma abubuwan da za ka kula da su a cikin yake- yaken, akwai addini a ciki,” inji shugaban.

Ya kara da cewa akwai wasu mutane da ke son ganin al’ummar Najeriya sun fada cikin rudani da tashin hankali ta fuskar addini da kabilanci da kuma bangaranci ta hanyar furta munanan kalamai na batanci da kuma cusa kiyayya. A cewarsa, jihohi irin su Binuwai da Taraba sun sami kansu a cikin wadannan matsalolin. Saboda haka sai ya ce masu son hargitsa Najiriya ta Arewa suna fakewa da batun makiyaya ke aiwatar da kashe-kashen da ake yi a wadancan jihohin amma sun mata da irin mutanen da sojoji ke kamawa dangane da kashe-kashen, wadanda babu makiyaya ko daya, sai makiyayan da ake kashewa tare da dabbobinsu. Ya kara da cewa ko a karshen makon da ya gabata, a kan iyakar jihohin Nasarawa da Biniwai, an kashe shanu saba’in da uku tare da kashe makiyaya biyu amma ba wanda ke maganar saboda kawai wata manufa ta daban ko kuma a ce akwai lauje cikin nadi.

Daga karshe kungiyar ta yi gargadi cewa mutane irinsu Fani Kayode da masu irin manufarsu, ba a bin da suke so illa su mayar da Najeriya irin matsayin kasashe irin su Libiya da Ruwanda da Sudan ta Kudu da kuma Yugoslabiya, kuma ya ce a shirye suke su fitar da irin kalar kowa a gane su, domin su burinsu a zauna lafiya.