✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana gwabza fada tsakanin sojoji da Boko Haram a Borno

Sun shafe sama da sa'a uku suna musayar wuta babu kakkautawa a garin Damasak

Rahotanni daga Jihar Borno na cewa a halin yanzu ana gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da mayakan Boko Haram a garin Damasak.

Majiyarmu ta tsaro ta ce sojoji sun ja daga suna kokarin fatattakar mayakan kungiyar ne bayan da suka shiga garin suna harbi kan mai uwa da wabi suna kone-kone.

Wani babban jami’in tsaron sa-kai na CJTF, da ya tabbtar wa Aminiya cewa an shafe awa uku ana musayar wuta babu kakkautawa ya ce, “Mu taya sojoji da addu’a su samu murkushe shaidanun nan, Boko Haram sun sake dawowa Damasak, bayan harin da suka kai ranar Asabar; A taya sojojin da addu’a.”

Aminiya ta kawo rahoto cewa a ranar Talata, mayakan kungiyar Boko Haram sun kwace garin suka kafa tutarsu, bayan da suka kuma kona caji ofis da cibiyoyin hukumomin agaji da asibiti da makaranta da gidaje da shaguna.

Majiyar tsaron da muka tuntuba kan yakin da ya kaure a safiyar Laraba ta ce, ­“Ina tabbatar maka cewa yanzu garin Damasak yana hannun sojoji, amma ana ci gaba da musayar wuta.

“Ka san a cikin kwanakin nan ’yan ta’adda sun kai hari a Damasak, amma ba za su yi nasara ba saboda sojoji sun yi tsayuwar daka domin su kare fararen hula”.