✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zanga-zanga a Spain kan dawowar tsohon Sarki Juan Carlos

Ana zargin tsohon sarkin da aikata almundahana ta kudade masu tarin yawa.

Daruruwan mutane ne suka yi zanga-zangar adawa da komawar tsohon Sarkin Spain Juan Carlos gida, wanda ya koma kasar daga Hadaddiyar Daular Larabawa, bayan shafe shekara biyu da gudun hijira.

Kakakin gwamnatin Spain, ya ce akalla mutane 300 suka gudanar da zanga-zangar kusa da fadar sarkin da ke birnin Madrid.

Sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna bacin ransu saboda zargin cin hanci da kuma halarta kudaden haramun da ake masa.

A ranar Litinin ake saran tsohon sarkin zai ziyarci dansa, Sarki Felipe na 6 kafin komawa Daular Larabawa, inda ya ke ci gaba da zama.

Gwamnatin Firaminista Pedro Sanchez na ci gaba da dakon bayanai kan dalilin da ya sa Juan Carlos, ya sauka daga karaga a 2014 domin nada dansa.