✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi watsi da ayyuka 150 da aka biya kudi

An bankado aiki 150 da aka yi watsi da su bayan an biya ’yan kwangila kudadensu har da karin iliyan biyar-biyar a Hukumar Neja Delta…

An bankado aiki 150 da aka yi watsi da su bayan an biya ’yan kwangila kudadensu har da karin iliyan biyar-biyar a Hukumar Neja Delta NDDC.

Likin ya tashi ne a binciken Darekta Janar din NDDC Farfesa Pondei Kemerbrandikumo kan kashe Naira biliyan 90.4 da ba sa cikin kasafin ma’aikatar a cikin shekara biyu (2009 zuwa 2011).

Rahoton Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya (AuGF) ya ce, “Bayanan Sashen Kula da Ayyuka na NDDC sun nuna an yi watsi da aiki 150 a yankin Neja Delta alhali an biya ‘yan kwangilar biliyan N23.215”, inji Kwamitin Majalisar Wakilai kan Neja Delta.

Rahoton AuGF din ya kuma nuna yadda NDDC ta rika biyan karin Naira biliyan biyar-biyar a kan kudaden kashi 77 na ayyukan, ta kuma kasa karbo kudaden.

Da yake amsa tambayoyi kan karya dokar da Majalisar ta ce dole a hukunta, Darke Janar din na NDDC ya amsa laifin kashe biliyan 90.4 din da ba sa cikin kasafin kudin.

Sai dai ya ce hakan ta faru ne saboda jinkirin da aka samu na amincewa da kasafin kudin hukumar a shekara biyun da ’yan majalisar ke bincike a kai.

Kamitin Majalisar ta umarci NDDC ta gabatar mata da dukkan takardun shaidar banki na kudaden da ta biya ’yan kwangilar da dangoginsu da kuma bayanan tsoffin darektocinta daga 2009 zuwa 2011.