✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi sama da fadi da tallafin noman shinkafa a Filato

Manoman shinkafa na zargin RIFAN da karkatar da kayan da gwamnati ta bayar

Manoma na zargin shugabanin Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) Reshen Jihar Filato da tatsar su da kuma yin sama da fadi da kayan tallafin noma da Gwamnatin Tarayya ta ba su.

Manoman shinkafar na zargin shugabaninsu sun yi ruf da ciki da irin shuka, takin zamani, magungunan feshin da sauran kayan noma da suka karbo da sunan manoman amma suka ki rabawa.

Don haka suka bukaci Gwamnatin Tarayya ta kawo musu dauki wurin tabbatar da an fito da kayan da ta bayar an kuma raba musu yadda Gwamnatin ta ce.

Daya daga cikin manoman, Alhaji Sule Yusuf, ya ce duk da cewa ya yi rajista da RIFAN kamar yadda ake bukata, har yanzu babu abin da aka ba shi na kayan noma.

Shi ma wani manomi, Paule Talmuk, ya koka da cewa ana cutar manoman shinkafa a Jihar Filato a wurin rabon injinan noma.

“Shugabanninmu na RIFAN na cutar mu; Suna amfani da sunayenmu da bayananmu su karbo abubuwa a madadinmu amma kuma sai su karkatar da su,” inji shi.

Aliyu Musa Sura, shi ma manomi ne, ya ce yaudarar su kawai ake yi da rabon kayan noman da Gwamnati ta bayar.

Domin “sai a sa mutum ya yi rajista da kungiyar, ya kuma cika dukkanin ka’idojin, amma idan aka zo maganar rabon kayan sai a yi ta kawo matsaloli.

“Wannan dabi’ar za ta kawo cikas ga kokarin Gwamnatin Tarayya na na ganin ana noma wadataccen abinci a kasar nan,” inji manomin.

Aminiya ta nemi ji daga bangaren RIFAN, amma Shugabanta na Reshen Jihar Filato, Joshua Bitrus, ya ki yin bayani game da zargin da manoman shinkafar ke yi.

“Ya kamata in san wadanda suke yin wannan zargin kafin in mayar da martani,” inji shi.