✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi karon batta tsakanin makiyaya da manoma a Kwara

An yi wa wasu makiyaya da ’ya’yan wani manomi biyu jina-jina.

Rashin fahimtar juna da ya janyo sa’insa kan hakkin mallakar filayen kiwon dabbobi ya auku tsakanin makiyaya da manoma, inda ya kai ga an zubar da jini a Jihar Kwara.

A cewar mai magana da yawun Hukumar Tsaro da Civil Defence a Jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi, ya je sa’insar ce ta kai ga an yi amfani da adduna da sauran makamai a yayin da bangarorin biyu suka hau dokin zuciya.

Ya ce an yi wa wasu makiyaya da ’ya’yan wani manomi biyu jina-jina a sakamakon karon battar da aka yi.

Sai dai ko shakka babu irin wannan rikici tsakanin makiyaya da manoma musamman a kan gonaki da burtalan kiwo ba kan shi farau ba.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da neman mafitar rikicin makiyaya da manoma, inda hankali ya fi karkata a zuciyar mahukuntan Najeriya na kare tsarin kiwon gargajiyar shekaru aru-aru a kasar.