✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da samari ’yan gida daya a Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba wa wasu samari ’yan gida daya a unguwar Tsallaken Dogo da ke Rigachikun a Kaduna. Dab da…

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba wa wasu samari ’yan gida daya a unguwar Tsallaken Dogo da ke Rigachikun a Kaduna.

Dab da Azahar ne a ranar Alhamis ’yan bindiga suka kutsa gidan iyayen samarin, suka tisa keyarsu, sannan suka rika harbe-harbe a hanyarsu ta tafiya da samarin.

“Shekarunsu ba su kai 20 ba; hankalinmu ya tashi domin tun da aka tafi da su ba mu kara jin labarinsu ba,” inji wani mazaunin unguwar.

Mazauna unguwar sun ce kimanin shekara guda ke nan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a unugwar.

Wakilinmu ya kira kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kadu, ASP Mohammed Jalige, game da lamarin, amma ya ce masa yana halartar wani taro, amma duk da haka zai bincika.