✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da matar shugaban Jam’iyyar APC a Neja

A kwanakin baya, wasu fusatattun matasa sun farmaki tawagar shugaban jam'iyyar.

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da matar Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukamar Magama a Jihar Neja, Alhaji Usman Baffa Ibeto.

Wata majiya daga makusantan Baffa ta bayyana cewa, an yi garkuwa da Habiba ne da asubahin ranar Litinin inda ’yan bindigar suka shiga har cikin gidansa da ke yankin Tunga a Minna, suka yi awon gaba da ita.

“Zuwa yanzu dai ba mu san halin da take ciki ba, kuma ba wanda ya kira waya don tattaunawa da shi, muna dai rokon Allah ya kubutar da ita cikin aminci.

“Lokacin da abin ya faru Baffa ba ya gari domin ya yi tafiya, amma mun gaggauta sanar da jami’an tsaro kan faruwar lamarin,” inji majiyar.

Bayanai sun nuna cewa ko a kwanakin baya, wasu fusatattun matasa sun farmaki tawagar Baffan a lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC a jihar, amma ya tsallake rijiya da baya.