✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da dan Majalisar Dattawa

Lamarin ya faru da Sanatan ne a kan hanyarsa ta zuwa gona.

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da Sanata Dickson Imasogie,  mai wakiltar mazabar Edo ta Kudu a Majalisar Dattawa.

Rahotanni sun ce da sanyin safiyar Litinin ne wasu mutane dauke da makamai suka yi awon gaba da sanatan a kan hanyarsa ta zuwa gona a kan titin Agbor a Jihar.

Bincike ya gano cewa an sace Sanata Imasogie na jam’iyyar PDP ne a lokacin da yake tare da direbansa da kuma wani mutum.

Ko da muka tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Edo, Bello Kongtons, kan lamarin, ya ce ba shi da masaniya.

Har zuwa lokacin da muka hada wannan rahoto babu wani cikakken bayani dangane da wadanda suka yi garkuwa da Sanata Imasogie, kuma ba su tuntubi iyalansa dan Majalisar Dattawan ba.