✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi artabu tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar Iraki

Masu zanga-zanga a Iraki sun kara arangama da jami’an ‘yan sanda a binrin Baghdad, a daidai lokacin da suke cika shekara daya da zanga-zangar kin…

Masu zanga-zanga a Iraki sun kara arangama da jamian yan sanda a binrin Baghdad, a daidai lokacin da suke cika shekara daya da zanga-zangar kin jinin gwamnati mai ci.

A ranar Litinin ’yan sanda suka tarwata dubban masu zanga-zangar ta hanyar harba musu hayaki mai sa hawaye.

Bangarorin sun yi dauki ba dadi ne s daidai lokacin da masu zanga-zangar ke kona tayoyi da jefe-jefe a kan gadar Al-Jumhuriyah, da ake bi a tsallake kogin Tigris, zuwa yankin Green Zone.

Hanyar Green Zone na cike da matakan tsaro, kuma wuri ne mai ofisoshin jami’an gwamnati, da na jakadacin Amurka.

Idan ba a manta ba, masu zanga-zangar da suka gudanar a bara, sun mamaye manyan garuruwa da ke Kudanci Iraki inda mabiya akidar Shi’a ke da rinjaye.