✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ware kwanaki 7 don farautar ‘yan ta’adda a Edo

Rundunar soji a jihar Edo ta ware kwanaki bakwai domin farauta 'yan ta'addar da suka addabi jihar.

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya roki jami’an tsaro a jihar su dawo da dokar hana fita don maganin ayyukan ’yan ta’adda.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin Kwamandan Rundunar Soji ta 2 a jihar, Manjo Janar Anthony Bamidele Omozoje.

“Yanzu dole mu sake dawo da dokar kulle daga 10 na dare zuwa 6 na safe; Duk wanda aka samu a waje lokacin dokar zai fuskanci hukunci mai tsanani.

“Za mu yi amfani da kwanaki bakwan wajen kama wadannan bata-garin sannan a dawo da makaman da suka sace daga hannun jamian tsaro”, cewar Obaseki.

Gwamnan ya ba wa rundunar sojin tabbacin hadin kai da kuma tallafi don ganin an dakile ayyukan taaddanci da suka addabi jihar tun bayan kammala zanga-zangar #EndSARS.

Obaseki ya ce hakan aka yi a jihohin Kwara, Oyo, Ekiti da Osun kuma duk an samu kyakykyawan sakamako.

A cewarsa bayan kammala farautar ’yan ta’ddar da suka damu jihar, za su duba nasarar lamarin kafin daukar mataki na gaba.