✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare matashin da ya yi luwadi da yaro dan shekara 10 a Kano

Mutumin da ake zargi ya yaudari karamin yaron ya kai shi har gidansa.

Wata Kotun Majistire a Jihar Kano ta bayar da umarnin garkame wani matashi mai shekara 35 a gidan dan kande kan zarginsa da aikata da yin luwadi da wani yaro dan shekara 10.

Kotun da ta bayar da wannan umarni a Larabar da ta gabata, tana zargin mutumin da ke zaune a Unguwar Kofar Waika da laifin zakke wa wani karamin yaro.

Lauya mai shigar da kara a gaban kotu, Asma’u Ado, ta ce wanda ake zargin ya aikata laifin da ake tuhumarsa a ranaer 5 ga watan Agusta a Unguwar da yake mazauni.

Asma’u ta ce da misalin karfe 10 da rabi na safiyar wannan rana ce mutumin da ake zargi ya yaudari karamin yaron ya kai shi har gidansa inda ya rika zakke masa ta dubura.

A cewarta, wannan laifi ya saba wa sashe na 284 na kundin final kot, sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito.

Alkalin Kotun, Majistire Sa’ad Datti, ya bayar da umarnin tsare wanda ake tuhuma a gidan kaso, inda kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Satumba.