✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin kasa makare da fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna ya taka ‘bam’

Ana harsashen jirgin ya dauko fasinjoji sama da 700 kafin lamarin ya faru

Wani jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna makare da fasinjoji ya taka bam din da aka dasa a kan titinsa a kusa da garin Katari da ke Jihar Kaduna.

Aminiya ta gano cewa jirgin wanda ta tashi daga tashar jiragen kasa ta Idu da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ya taka bam din ne kimanin mintina 30 kafin ya isa tashar Rigasa a Kaduna.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma Aminiya ta gano an tura jami’an tsaro zuwa wajen don ceto fasinjojin.

“Babu cikakken sabis din waya a wajen da lamarin ya faru ballantana mu san me ya faru a can, dole sai jami’an da muka tura sun dawo kafin mu san hakikanin abin da ya faru,” inji wata majiya daga jami’an tsaro a Kaduna.

“Abin da muka sani shi ne an dasa bam a kan titin jirgin, kuma titin ya sauka daga kan layinsa. Amma ba za mu iya hakikance ko wani ya samu rauni ba,” inji shi.

Sai dai wasu majiyoyin sun ce maharan sun rika harbi kan mai uwa da wabi, a kokarinsu na kwashe fasinjojin.

Ana harsashen jirgin ya dauko fasinjoji sama da 700 kafin lamarin ya faru.