✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tashi wasan Najeriya da Ghana babu ci

Tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta tashi babu ci a wasan da ta fafata da takwararta ta Black Stars ta Ghana, a gasar…

Tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta tashi babu ci a wasan da ta fafata da takwararta ta Black Stars ta Ghana, a gasar neman cancanta buga Kofin Duniya da za a yi bana a kasar Qatar.

An buga wasan ne da maraicen Juma’a, a filin wasa na Baba Yara da ke birnin Kumasi a kasar ta Ghana.

Ana sa rana sake buga wasan a filin wasa na kasa na Moshood Abiola da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ranar Talata, 29 ga watan Maris, 2022, da misalin karfe 6:00 na yamma.

Duk kasar dai da ta samu nasara za ta kasance cikin daya daga cikin jerin kasashe biyar din da za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniyar da za a buga a tsakiyar wannan shekarar.