✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sayar da takalmin Michael Jordan kan Dala miliyan 2.2

Takalmin ya yi farin jini ga masu bibiyar kwallon kwando ta Amurka.

An sayar da takalmin da Michael Jordan ya sa a gasar kwallon kwando ta Amurka (NBA) a kan Dala miliyan 2.2.

An yi gwanjon takalmin da ake kira Sneakers a ranar Talata kamar yadda Kamfanin Gwanjon Sotheby ya sanar.

Zakakurin dan wasan ya sa takalmin da ake kira Air Jordan a wasa na biyu a 1998 karawar karshe da ya lashe kofi na shida na NBA.

Wannan cinikin da aka yi a Intanet ya dora Jordan a matakin farko da aka sayi kayan dan wasa mafi tsada a duniya.

Ya zarce yawan kudin takalminsa da aka sayar a watan Satumban 2021 kan Dala miliyan 1.5.

A bara aka sayar da wata rigar da ya yi amfani da ita a wasan kwallon kwando kan Dala miliyan 10.1, kudin da aka biya mafi tsada ga kayan dan wasa a lokacin da aka yi gwanjon.

Jordan ya sa takalmin a zagaye na biyu a wasan da Chicago Bulls ta yi nasarar cin Utah Jazz 93 da 88 a ranar 5 ga Yunin 1998.

Jordan ya ci wa Bulls maki 37 a fafatawar.

Kudin da aka sayi takalmin ya haura hasashen da kamfanin gwanjo na Sotheby ya yi na Dala miliyan 2, amma bai kai Dala miliyan 4 da aka ce za a iya samu ba.

Kamfanin gwanjon ya ce Jordan da kansa ya sa hannu a kan takalmin, sannan ya bai wa wani yaro mai dauko kwallo idan ta fita daga fili kyauta.

Sai dai Sotheby bai fayyace wanda ya mallaki takalmin ba mai lamba 13, bai kuma sanar da wanda ya saya ba.

Takalmin ya yi farin jini ga masu bibiyar kwallon kwando ta Amurka, takalmin mai launin baki da ja, Jordan ya rika sawa a kakar da yake lashe kofin NBA.

Jordan, wanda yanzu yake da shekara 60 a duniya ya yi wasa a Kungiyar Bulls, inda ya lashe kofin NBA shida, sannan ya yi ritaya.

Daga baya ya koma buga kwallon kwando a Amurka a 2001, wanda ya yi kaka biyu a Washington Wizards.