✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu rudani a kotu yayin shari’ar yaran Sunday Igboho

Kotu ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 4 ga Agusta, 2021.

Kotu ta dage sauraron shari’ar yaran Sunday Igboho mai tarasahin neman kafa karar Yarabawa da suke tsare a hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS).

A ranar 1 ga watan Yuli ne DSS ta tsare yaran Sunday Igboho 12 a wani samame da takai musu a maboyarsu da ke gidansa a garin Ibadan, Jihar Oyo, inda aka dauki lokaci ana luguden wuta.

Jami’an hukumar sun kwato miyagun makamai da kayan tsubbace a maboyar yaran na Igboho, wanda Gwamnatin Tarayya take nema ruwa a jallo.

Hukumar ta gurfanar da takwas daga cikinsu a gaban Babbar Kotu Tarayya da ke Abuja ne a ranar Litinin, amma aka samu rudani kan sunayensu da lauyan ya gabatar wa kotun.

A kan haka ne lauyan da ke kare su, Pelumi Olagbenjesi, ya bukaci alkalin Kotun, Mai Shari’a Obiora Egwuatu, ya umarci hukumar ta kawo ragowar mutanen su halarci zaman kotun na gaba.

Tun da farko lauyan na yaran Igbohon ne nemi ba shi karin lokaci domin yin gyara a sunayen, ya kuma shigar da wasu bayanan da ya tattaro bayan ganawarsa da su a ofishin hukumar.

Ganin lauyan DSS bai kalubalanci bukatar ba, sai alkalin ya dage zaman zuwa ranar Alhamis, 4 ga Agusta, 2021.

A ranar 23 ga watan Yuli Kotun ta umarci DSS ta gurfanar da wadanda ake zargin a ranar Alhamis 29 ga watan, amma hakan bai samu ba.

Sunday Igboho, wanda Najeriya take neman ruwa a jallo yana tsare a kasar Jamhuriyar Benin inda yake fuskantar shari’a bayan ’yan sanda kasa da kasa sun kama shi a ranar 19 ga watan Yuli yana kokarin barin kasar tare da matarsa Bajamushiya, zuwa kasar Jamus.