✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kwaso karin ‘yan Najeriya 159 daga Libya 

Wadanda aka kwaso sun iso gida Najeriya da yammacin ranar Talata.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta sake karbar wasu ‘yan Najeriya 159 da aka dawo da su gida bayan sun makale a Kasar Libya.

NEMA ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba a Legas.

NEMA ta ce da yammacin ranar Talata ne mutanen da suka dawo suka isa filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Ikeja, babban birnin Jihar Legas.

An kwaso su a cikin jirgin Al Buraq Air Boeing 737-800 mai lamba 5A-DMG.

NEMA ta ce wadanda aka dawo da su sun hada da maza 71 da mata manya 74 da kuma jarirai 14.

Mista Mustapha Ahmed, Darakta-Janar na NEMA, ne ya karbi wadanda suka dawo a madadin Gwamnatin Tarayya kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ya shawarce su da su dau izina da abubuwan da suka faru da su kuma su kasance masu bin doka da oda.

Sanarwar ta ce, Ahmed, ya samu wakilcin Mista Ibrahim Farinloye, Kodinetan ofishin hukumar na Legas.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta jajirce wajen ganin ‘yan Najeriya ba su makale a kasashen ketare ba.