✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace Shugaban makaranta a Batsari

Maharan sun ce a daina kiran su za su kira a lokacin da suke bukata.

Ana zargin ‘yan daban daji masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Shugaban Makarantar Sakandaren garin Ruma da ke kan hanyar Batsari zuwa Jibiya.

Majiyoyi sun ce Shugaban makarantar mai suna Sani Sa’idu Batsari, ya yi kicibis da maharan a hanyarsa ta zuwa garin Batsari bayan ya taso daga garin Ruma a ranar Juma’a.

Wani dan uwansa mai suna Saminu Mayen Tea ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun sace Shugaban makarantar da rana kuma ba su tafi da babur din sa ba.

Ya ce sun tuntubi iyalan nasa amma ba su ce ga wani abin da suke bukata ba daga gare su ba.

Sai dai ko da aka kira su, sun ce a daina kiran su za su kira a lokacin da suke bukata.

Sani Sa’idu Batsari

Wakilin Aminiya ya ruwaito yadda sata da kisa da kuma yin garkuwa da mutane suka fara zama ruwan dare a wannan yanki, har kusan ya fara zame wa mutane jiki.

A makon jiya, Aminiya ta ruwaito yadda jami’an tsaro suka yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga hudu suka kuma kama wasu a wani gari da ake kira Dangeza a wannan yankin.

Har zuwa lokacin rubuta wannan labarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina SP Gambo Isa bai tabbatar da labarin ba inda ya ce sai ya tuntubi babban jami’in ’yan sanda na yankin zai yi karin haske.