✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe wani katafaren shago a Abuja saboda fargabar tsaro

Muna bai wa abokan huldarmu hakuri.

An rufe fitaccen rukunin shagunan Jabi Lake da ke Abuja, bayan gargadin yiwuwar kai hari babban birnin kasar da wasu kasashen ketare suka yi.

Akalla kasashe biyar ne dai suka fitar da gargadin ga ‘yan kasarsu da su guji tafiye-tafiye zuwa Abuja.

A kunshin sanarwar da Hukumomin gudanarwar rukunin shagunan Jabin suka fitar, sun nemi afuwar kwastomominsu kan cikas din da hakan ya haifar.

“Ga Kwastamominmu masu daraja, za a rufe  Jabi Lake a yau, Alhamis, 27 ga Oktoba 2022.

“Wannan mataki an dauke shi ne domin kare lafiyar dukkan ma’aikata da abokan huldarmu.

“Hukumar gudanarwar na ci gaba da nazarin yanayin tsaro da tuntubar hukumomin da abin ya shafa kan lamarin, kuma za su sanar da ku lokacin da za a sake bude kasuwar da zarar komai ya daidaita.

“Muna fatan za mu samar muku da ingantacciyar hanyar siyayya nan ba da jimawa ba.”, a cewar sanarwar.

Jami’an tsaro dai na kara sanya ido a babban birnin tarayya Abuja da kewaye domin dakile hare-haren.

Kazalika an kuma kama wasu da ake zargi da ta`addanci, a sintiri kare asarar rayukan al`umma a Abujan.

Aminiya dai ta ruwaito yadda jami’an tsaro ke kokarin dakile munanan hare-haren da ake zargin ‘yan ta’adda na shirin kaiwa Abuja da kewaye.