✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe Kwalejin Nuhu Bamalli da ke Zariya

Har yanzu ba a san adadin mutanen da aka yi awon gaba da su ba.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba da umarnin rufe Kwalejin Nuhu Bamalli da ke garin Zariya a jihar, biyo bayan sace wasu dalibai da malamai da wasu ’yan bindiga suka yi a ranar Alhamis.

Har ya zuwa yanzu ba a san adadin mutanen da ’yan bindigar suka sace a Kwalejin ba.

  1. Zamfara: An dakatar da Sarkin Zurmi kan ayyukan ’yan bindiga
  2. Buhari ya mika karin kasafin biliyan N895 ga Majalisa

Kai hari makarantu tare da sace dalibai da malamai ba sabon abu bane a Jihar Kaduna, inda a cikin shekarar nan ’yan bindiga sun yi garkuwa da daliban Kwalejin Gandun Daji da ke Afaka da kuma dalibai da ma’aikatan Jami’ar Greenfield duk a jihar ta Kaduna.

Matsalar garkuwa da mutane na ci gaba da kamari a yankin Arewa maso yammancin Najeriya, musamman a Jihohin Kaduna, Katsina, Sakkwato, Zamfara da Kebbi.

Ita ma Jihar Neja na fama da matsalar masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga da ke ci gaba da kai hare-hare.

A baya-bayan nan ma sai da wasu ’yan bindiga suka sace daliban Islamiyya a garin Tegina da ke jihar, wanda adadinsu ya haura 100.