✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe Jami’ar Legas saboda annobar Coronavirus

Majalisar Gudanarwar Jami’ar Legas, ta umarci daliban da ke zama a dakunan kwananta da su fice bayan samun wasu dalibai da suka harbu da cutar…

Majalisar Gudanarwar Jami’ar Legas, ta umarci daliban da ke zama a dakunan kwananta da su fice bayan samun wasu dalibai da suka harbu da cutar Coronavirus.

Aminiya ta samu cewa matakin na zuwa ne bayan wani taron gaggawa da Majalisar ta gudanar a ranar Laraba wanda Shugaban Jami’ar, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe ya jagoranta.

Farfesa Ogundipe ya ce sun yanke matakin hakan ne a yayin taron gaggawa da ya jagonta domin yin nazari kan halin da ake ciki.

A yayin taron ne Majalisar ta yanke hukuncin dakatar da karatu a jami’ar har zuwa ranar 26 ga watan Yuli, inda za ta ci gaba da gudanar da shi daga nesa ta hanyar intanet.

Wani dalibi a sashen Nazarin Sadarwa, ya shaida wa wakilinmu cewa, Shugaban Kula da Harkokin Dalibai ya umarce su da su fice daga jami’ar kuma malamai za su ci gaba da karantar da su ta hanyar yanar gizo.

Tuni dai Cibiyar Lafiya ta jami’ar ta sanar da samun karuwar marasa lafiya kuma alamu sun nuna cewa suna dauke da kwayoyin cutar Coronavirus.

Sai dai Cibiyar ta ce tana daukar matakan da suka dace domin kare lafiyar dalibai da ma’aikatan da ke cikin jami’ar.

Aminiya ta ruwaito cewa, annobar cutar Coronavirus ta sake barkewa karo na uku a Jihar Legas kamar yadda Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar a ranar Lahadi.