✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karon farko, an rantsar da mata 98 a matsayin alkalai a Masar

An kafa tarihi a kasar bayan rantsar da mata 98 a matsayin alkalai.

Kasar Masar ta nada mata 98 a matsayin alkalai a daya daga cikin manyan hukumomin shari’ar kasar, wato Majalisar Kula da Harkokin Shari’a.

An nada alkalan ne a gaban Alkalin Alkalan Majalisar, Mohammed Hossam el-Din, a wani taro a birnin Alkahira na kasar, a ranar Talata.

Wanann na zuwa ne bayan Shugaba Abdul-Fattah Al-Sisi, ya yi kira ga mata su shiga manyan hukumomin shari’ar kasar.

Tuni mutane da dama ciki har da masu rajin kare hakkin mata suka fara jinjinawa El-Sissi, kan kiran da ya yi na mata su shiga harkar shari’ar kasar.

Tun bayan kafa majalisar a 1946 dai, maza ne kawai ake nadawa kuma ba a amincewa da mata masu son aiki da majalisar.

Hakan ya sa mata da dama daga ciki da wajen kasar suka dinga sukar tsarin a shekarun baya.