✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da Gwamna Obaseki a karo na biyu

  An rantsar da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shuaaibu a wani sabon wa’adi karo na biyu. Lauyar koli ta jihar, Mai…

 

An rantsar da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shuaaibu a wani sabon wa’adi karo na biyu.

Lauyar koli ta jihar, Mai Shari’a Esther Edigin ce ta rantsar da Obaseki da mataimakinsa da misalin karfe 12.00 na ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamban 2020.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin rantsuwar da aka gudanar a farfajiyar filin wasanni ta Samuel Ogbemudia da ke birnin Benin sun hada da wasu Gwamnonin jam’iyyar PDP ciki har da Nyesom Wike na jihar Ribas, Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, Ifeanyi Okow ana jihar Delta da kuma Duoye Diri na jihar Bayelsa.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus na cikin wadanda suka albarkaci taron yayin da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya samu wakilcin wasu manyan jami’an gwamnati.

Gwamna Obaseki wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP sakamakon hana shi tikitin takara, ya kayar da dan takarar da jam’iyyar APC ta tsayar, Osagie Ize-Iyamu a yayin zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.