✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwato ma’aikata da aka yi garkuwa da su a Abuja

Hankula sun tashi bayan da aka kai wa jami’an Hukumar Yankin Birnin Tarayya da ke Gaduwa hari. Rahotanni na nuna yadda maharan suka jikkata jami’an…

Hankula sun tashi bayan da aka kai wa jami’an Hukumar Yankin Birnin Tarayya da ke Gaduwa hari.

Rahotanni na nuna yadda maharan suka jikkata jami’an hukumar yayin da aka yi garkuwa da wasu.

Daga baya dai an sako jami’an bayan tawagar ceto ta ’yan sanda karkashin jagorancin kwamishinan ’yan sanda Bernard Igwe sun yi wa wurin musu dirar mikiya.

Hadimin Ministan Birnin Tarayya na musamman da ke sa ido da kuma tabbatar da doka Ikharo Attah ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce “Wasu daga cikin jami’an sun gano wasu haramtattun gidaje da dama da ’yan bindiga ke jibge muggan makamai a ciki”.

Da yake yaba wa wasu matasa da suka ba wa hukumar gudummawar shawo kan matsalar, Attah ya ce ba don gudummawarsu da ta jami’an tsaro ba, da bata-garin sun yi barna mai yawa.

Wasu daga cikin wadanda aka sacen an ji musu mummunan rauni aka, wasu kuma an kai su asibiti.