✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori ma’aikata 286 a Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Kaduna

Hukumar ta ce ta kore su ne bayan ta gano akasarinsu da takardun bogi suke amfani.

Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Kaduna (KADSWAC) ta tabbatar da korar ma’aikatanta kimanin 286 bayan wani aikin tantancesu da ta gudanar.

Shugaban hukumar, Sanusi Maikudi ne ya tabbatar da hakan yayin wata tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Kaduna ranar Talata.

Ya ce sun dauki matakin ne bayan aikin tantancewar da suka yi musu, inda suka gano akasarinsu da takardun bogi suke amfani.

Ya ce, “ A sakamakon tantancewar, mun gano ma’aikatan da ba sa zuwa aiki da wadanda suka yi karyar shekaru da marasa lafiya da kuma wadanda aka dauka ba bisa ka’ida ba.

“Kaso mafi tsoka daga cikinsu na amfani ne da takardun bogi, wanda yin hakan kuma babban laifi ne, wannan ne ya sa muka kore su.

“Za mu gudanar da bincike a kansu, wadanda muka gano ba su da laifi mu kyale su, masu laifi kuma su fuskanci hukunci daidai da girman laifin nasu.

“Daga ciki, wadanda muka samu da kananan takardun karatu, ko almundahanar kudi ko karya dokokin aiki mun kore su daga aiki, wasu kuma mun yi musu ritayar dole,” inji shi.

Maikudi ya ce daukar matakin ya zama wajibi la’akari da muhimmancin samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’umma.

“Gwamnatin Jiha ta kashe makuden kudade wajen inganta harkar samar da ruwan sha, abin da kawai muke bukata shi ne kwararrun ma’aikata masu kwazo da za su tafiyar da akalarta don amfanin al’umma.

“Babban aikinmu shi ne mu tabbatar da lafiyar al’umma mu kare su daga kamuwa da cututtuka masu alaka da ruwan sha,” inji shugaban hukumar. (NAN)