✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe wani kwamandan bijilanti a Kano

Wasu masu tayar da zaune tsaye sun hallaka kwamandan ’yan bijilati na unguwar Danbare da ke Karamar Hukumar Kumbutso a Jihar Kano, Mansur Ibrahim. Ana…

Wasu masu tayar da zaune tsaye sun hallaka kwamandan ’yan bijilati na unguwar Danbare da ke Karamar Hukumar Kumbutso a Jihar Kano, Mansur Ibrahim.

Ana zargin cewa wasu ne suka kira marigayin suka yaudare shi da cewar za su ba shi aikin gini a unguwar Kauyen Ta-Inna wanda da zuwansa wajen ya tarar da su dauke da muggan makamai, kuma kwatsam suka fara dukansa, lamarin da ya yi sanadiyar rasuwarsa.

Mai Unguwar Danbare, Sulaiman Ahmad, ya yi kira ga mahukunta da su zakulo wadanda ake zargi da aikata laifi.

Kwamandan ’yan sintiri a yankin, Abubakar Lawan ya bayyana cewa wadannan mutane da suke aikata irin laifin sun dauki rayuwar ’yan bijilanti ba komai ba.

Ya kara da cewa jami’an bijilanti na bayar da gudunmawa a unguwanni da ba za su misaltu ba.

Abubakar Lawan ya ce marigayin ya rasu ya bar mata da ’ya’ya kusan 15.

Ya kuma yi kira ga Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano da ya zurfafa bincike domin kamo wadanda ake zargi dan hukunta su.

Aminiya ta yi yunkurin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, amma hakan ya ci tura kawo wannan lokaci.