✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe soja a wurin kwato mutane daga hannun masu garkuwa

An kwato yara hudu a daura Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello.

Wani soja ya rasa ransa a yayin musayar wuta domin kwato wasu mutane da ’yan bindiga suka sace a kauyen Mil Goma da ke daura da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika a Karamar Hukumar Sabon Gari, Jihar Kaduna.

A ranar Litinin da misalin karfe 9 na dare ne ’yan bindiga kusan 30 dauke da manyan bindigogi suka kai hari a gidan wani a yankin na Mil Goma, inda suka yi awon gaba da matarsa da ’ya’yansa hudu, maza uku da mace daya.

Rundunar ’Yan Sanda na Musamman da ke Yaki da ’Yan Ta’adda da kuma Satar Mutane (IRT) da Baturen ’Yan Sandan yankin Samaru da sojoji da ’yan sa-kai sun kai daukin gaggawa zuwa garin.

A nan ne suka yi suka yi dauki ba dadi da ’yan bindigar wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwa wani soja, bayan an kai shi asibiti.

– An kubutar da mutum hudu

Bayanai sun tabbatar da cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kubutar da ’ya’yan magidancin su hudu daga hannun masu garkuwar, amma ’yan bindigar sun tsere da raunin harbin bindiga a jikinsu.

Wasu bayanai da muka samu na cewa an tsici gawar wani da ake zaton daya ne daga cikin maharan.

Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaron sun killace yankin da nufin ceto sauran wadanda ke hannun masu garkuwar da kuma cafke ’yan bindigar.

Wakilimu ya tuntubi mai magana da yawun Rundunar Horas da Kuratan Sojoji (Dafo) da ke Zariya, Laftanar Joy Abah, amma ta ce ba ta da labari, amma da zarar ta samu za ta sanar da mu halin da ake ciki.