A ranar Lahadin da ta gabata ce masu garkuwa da mutane da aka ce adadinsu ya kai 20, su ka bude wuta a kan matafiya a kan hanyar Abuja zuwa Lakwaja.
Lamarin wanda ya faru a kauyen Kwaita da ke tsakanin Abaji Gwagwalada da ke Birnin Tarayya Abuja, ya auku ne da misalin karfe 5:00 na yamma kamar yadda wadanda lamari ya rutsa da su suka shaida wa Aminiya.
Wani da ya tsira daga harin mai suna Kasim Akale da ya rasa dan uwa mai suna Yakubu Akale a harin, ya ce isowarsu wajen sai ’yan bindigar suka bude musu wuta kuma nan take mutum hudu a cikin motarsu kirar bas mai dauke da mutum 18 suka rasu. Ya ce bayan sun fito daga cikin motar da fasinjojin wasu motoci, wadansu daga cikinsu sun samu nasarar tsallakawa daya hannun da nufin neman tsira, amma sai wadansu ’yan bindigar suka sake dawo da su.
“Ta wannan hannun ne wanda ke da yanayin tsaunuka suka kora mu, sai dai mun samu nasarar kubuta a yayin tafiyar, ni da dan uwanwa da ya rasu daga bisani sakamakon bugun zuciya,” inji shi. Malam Kasimu Akale ya ce adadin wadanda suka rasu a harin sun dara wanda hukuma ta bayar saboda ’yan bindigar sun yi ta kashe duk wanda ya kasa ci gaba da tafiya sakamakon gajiya a yayin da suke kutsawa cikin dajin da su. Ya ce adadin wadanda a ka shiga da su dajin ya kai mutum 40.
“Wani matashi da aka ce tsohon soja ne shi ne ya kashe daya daga cikin ’yan bindigar, ya kuma kamo wani ya zo da shi kan hanya. A nan ne jami’an tsaro da suka zo daga baya suka wuce da wanda ya kamo,” inji shi.
Ya ce dan uwansa wanda Mataimakn Shugaban Makarantar Sakandare ce a garin Kubwa, Abuja, ya bar ’ya’ya 2 da matarsa, kuma an yi masa jana’iza a ranar Litinin da ta gabata.