✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 2 saboda kyamar addinin Islama a Iran

Sun jima suna wallafa ra’ayoyi na batanci da kuma yada kyamar addinin Islama.

Iran ta kashe wasu mutane biyu da ta yanke wa hukuncin kisa a baya, bisa laifin yada farfaganda ta nuna kyamar addinin Musulunci a shafukan intanet.

Iran ta kashe mutanen biyu ne da ta yanke wa hukuncin kisa a baya, bayan samunsu da laifin yin batanci ga addinin Musulunci.

Kamfanin Dillancin Labaran kasar mai suna Mizan ne dai ya wallafa labarin a shafinsa na yanar gizo a wannan Litinin din, amma ba tare da bayyana takaimaimen ranar da aka aiwatar da kisan ba.

Kamfanin ya nuna cewa, mutanen da aka aiwatar da kisan kansu, sun hada da Yousef Mehrdad da Sadrollah Fazeli Zare.

Haka kuma, sun jima suna amfani da shafukansu na yanar gizo a wallafa ra’ayoyi na batanci da kuma yada kyamar addinin Islama, laifukan da suka saba wa dokokin kasar ta Iran.