✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 2, an sace tsohon Kwamishina a Adamawa

'Yan bindigar sun yi awon gaba da shi a gidansa ranar Talata

’Yan bindiga sun sace tsohon Kwamishinan Gidaje da Tsare-tsare na Jihar Adamawa, Injiniya Idris Babangida a ranar Talata.

Rahotannin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kewaye gidansa da ke kauyen Bajabire a Karamar Hukumar Girei ta Jihar, inda suka harbe shi a kafa, sannan suka kashe mutum biyu tare da jikkata wasu da dama kafin su yi awon gaba da shi.

Wani dan uwansa ya bayyana wa Aminiya cewar wadanda suka sace shi sun bukaci a ba su Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansar shi.

“Abin da ya fi daga mana hankali a yanzu shi ne ya tsallake rijiya da baya a lokacin zaben fidda-gwani na jam’iyyar APC, wanda har yanzu ba a gano wanda suka kai masa harin ba,” inji dan uwan nasa.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Suleiman Nguroje, ya ce sun samu rahoton faruwar lamarin.

Ya kuma ce suna kokarin ganin an ceto shi daga hannun wanda suka sace shin.