✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe matar aure, an sace mutum 6 a Abuja

Kwana biyu a jere ’yan bindiga suka dauka suna kai hari a unguwar da ke Abuja

Wasu masu garkuwa dsa mutane sun shiga gida-gida sun kashe wata matar aure tare sa sace wasu mutum shida a yankin Kwali da ke Abuja.

Wani mazaunin yankin mai suna Yakubu Saidu, ya ce ’yan bindigar sun fara ne da shiga wasu gidaje biyu suka sace mutum biyu tare bude wuta cikin daren ranar Talata.

Daga nan suka shiga gidan wani dillalin motoci, mai suna, “Amma ba su same shi ba saboda ya tsere, amma sun yi awon gaba da kannensa maza biyu.”

A cewarsa, a ranar Laraba kuma ’yan bindiga sun sake zuwa yankin da misalin karfe 11:23 na dare suka kashe matar a lokacin da take kokarin tserewa.

Ya ce matar ’yar uwar wani dan kasuwa ne amma, “Sun kasa samun mijin matar saboda ya buya, amma sun sace matarsa ta biyu da kuma mutum biyu a gidan.”

Wasu daga cikinsu maharan sun shiga wasu gidajen suka yi garkuwa da mutum uku.

Ya bayyana cewar an birne matar kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.