✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mana mutum 89 cikin wata 3 —Al’ummar Apa

Kungiyar ta musanta cewar hare-haren na da nasaba da rikicin sarauta.

Kungiyar Raya Al’adu ta Al’ummar Apa ta ce mutum 89 ne mahara suka kashe a kauyuka 31 da ke Karamar Hukumar Apa ta Jihar Binuwai cikin wata uku.

Da yake jawabi ga manema labarai a Makurdi, shugaban kungiyar, Eche Akpoko, ya bayyana matsalar tsaro a yankin a matsayin babban tashin hankali.

Ya ce kauyukan da abin ya shafa sun hada da Oleoke-Ikobi, inda aka kashe mutum 40, sai kuma Ope-Ikobi da Ochi-Ikobi da Olugwu-Ikobi da Inowa-Ikobi da Olegoncha-Ikobi da Ijaha-Ikobi da kuma Imana-Ikobi.

Ya kara da cewar an kashe mutum 20 a fadin Ebugodo-Edikwu, Ankpali-Edikwu, Olegijamu-Edikwu, Olekele-Edikwu, Ukpogo-Edikwu, Edikwu-Icho da sauransu.

“A Ugbobi, an kashe mutum biyar ciki har da hakimin kauyen. A Odugbo, an harbe mutum takwas, yayin da aka kashe mutum biyar a Olegogba, sannan an kashe mutum daya a Akpete da Opaha. An kuma kai wa Akpanta da Iyapu hari inda aka kashe mutum biyu a kowannensu.”

Sai dai ya karyata labaran da ake ta yadawa cewa hare-haren da aka kai wa al’ummar Karamar Hukumar Apa sun faru ne sakamakon rikicin sarauta.

“Wannan labari hasashe ne da rashin tushe.

“Muna tabbatar da cewa dalilin wadannan hare-haren ba gaira ba dalili a kan mutanen Karamar Hukumar Apa ba gaira ba dalili!”

Akpoko ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihar da su hada hannu da hukumomin da abin ya shafa domin kai wa jama’a agaji.

Ya yi gargadin cewa za a iya tilasta wa jama’a su yi amfani da ’yancinsu na kare kansu, wanda hakan ka iya haifar da tabarbarewar doka da oda.

Aminiya ta ruwaito cewar Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya ce akalla mutane 134 ne wasu mahara suka kashe a cikin kwanaki biyar a wasu hare-hare da suka kai kauyukan Karamar Hukumar Otukpo, Apa da Guma na jihar.

Ortom, wanda ya yi magana da manema labarai a lokacin da ya ziyarci sama da mutum 36 da suka jikkata, wadanda galibi mata ne da kananan yara ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Binuwwi (BSUTH), ya bayyana hare-haren a matsayin abun takaici.