✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mahaifin dan kasuwa an sace shi a Birnin Tarayya

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan kasuwa tare da ’yarsa bayan sun kashe mahaifinsa a Yankin Babban Birnin Tarayya.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan kasuwa tare da ’yarsa bayan sun kashe mahaifinsa a Yankin Babban Birnin Tarayya.

Kafin wayewar garin Asabar ne maharan suka shiga unguwar Chitumu da ke yankin Zuba a Karamar Hukumar Gwagwalada suka yi wannan aika-aika.

Sakataren Hakimim Gwagwalada, Muhammad Liman, ya ce maharan sun wuce ne kai-tsaye zuwa gidan wani mai kasuwancin shanu, Isiaka Alhassan Dogara, inda “Da zuwansu suka dauke shu da wata ’yarsa mai shekara 14.

“Sauran ’yan bindigar da suka zagaye gidansa kuma suka harbe mahaifinsa, Alhassan Dogara wanda ya fito bayan jin koke-koken matan dan nasa.”

Ya kara da cewa maharan sun kuma harbi baffannin dan kasuwan su uku da suka kai masa dauki.

Ya bayyana cewa an garzaya da daya daga cikin mutanen da aka harba din zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada.