✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe kwamandojin Boko Haram 3 da mayakansu 27 a Sambisa

Mun rasa mayaka kusan 30, ciki har da kwamandojin mu uku.

Wasu hare-hare ta sama da jiragen yakin sojojin saman Najeriya na Super Tucano suka kai sun kashe kwamandojin Boko Haram uku a dajin Sambisa da ke Jihar Borno.

Harin na bama-bamai da aka kai a sansanonin Boko Haram guda hudu a ranar 1 ga watan Janairu, 2023, ya kuma kashe ’yan ta’adda 27, yayin da wasu 40 suka tsere zuwa cikin dajin da raunukan harbin bindiga.

Wani kwararre a fannin yaki da tayar da kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan ranar Talata a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Ya bayyana cewa, bayan sahihan bayanan sirri da aka tattaro kan ‘yan ta’adda a sansanoni hudu da ke shirin kaddamar da hare-hare a sansanonin soji da ke kusa da su, jiragen sojin suka yi wa sansanonin dirar mikiya, inda suka kashe mafi yawansu, ciki har da shugabannin su uku.

A cewarsa, sansanonin da aka kai harin sun hada da Bula Jitoye, Halka Kojoy, Halka Alai da Bulamaye a Karamar Hukumar Bama.

Ya ce: “Boko Haram ta fitar da wani faifan bidiyo na mintuna biyu da dakika 50, inda mayakanta a kan babura ke kona bukkoki da motoci tare da kashe wasu ’yan kungiyar IS da ke da’awar jihadi a Yammacin Afirka (ISWAP).”

Ya kara da cewa, hakan ya faru ne cikin kasa da sa’o’i 24, bayan wani kazamin fadan da aka shafe sa’o’i 14 ana gwabzawa tsakanin bangarorin biyu na ’yan ta’adda a Toumbun Allura da Kangar a kan iyakar kasar ta Nijar.

Makama, wanda ya bayyana hare-haren a matsayin “Yakin daukar fansa”, ya ce Ali Ngulde da wasu kwamandojin da suka hada da Abu Nazir, Muke, Ba’a Isa da kuma Malam Abubakar ne suka jagorance su.

Wata majiyar soji a Maiduguri ta kuma bayyana cewa, hare-haren hadin gwiwar na sama da na kasa ya biyo bayan kazamin fadan da ‘yan ta’addan suka yi a yankin.

Don haka majiyar ta kara da cewa, an kashe daya daga cikin kwamandojin, wanda ake kira Captain ko Likita, sakamakon harin da jiragen saman suka kai sansanin Bula Jitoye, inda ya kara da cewa: “An kashe sauran biyun, (ba a tantance sunayensu ba) a Halka Kojoye da Halka Alai.”

An ji daya daga cikin ’yan ta’addan a wata hanyar sadarwa da aka datsa, yana mai cewa: “Muna kashe ISWAP tare da kwace dukkan makamansu. Amma babbar matsalarmu ita ce, jiragen yakin soja suna kashe mu ma.

“A ranar 1 ga Janairu, 2023, mun rasa mayaka kusan 30, ciki har da kwamandojin mu uku.”